Zargin maita: Wata mata ta maka makwabtanta 3 kara kotu saboda suna kiranta da suna ‘mayya’

Zargin maita: Wata mata ta maka makwabtanta 3 kara kotu saboda suna kiranta da suna ‘mayya’

-Wata mata ta kai karar makwabtanta kotu a dalilin su na kiranta da suna mayya

-Aisha Idris ta shaidawa kotun shari'a cewa matan su uku wadanda suke zaune a gida daya da su sun sanya ita da mahaifiyarta a gaba

Aisha Idris mai shekaru 25 a duniya ta kai karar makwabtanta su uku gaban kotu ranar Laraba a sakamakon kiranta da suke yi da suna mayya.

Ga sunayen mutanen da Aisha ta kai kara kotun shari’a wadda ke zaune a shiyyar Magajin Gari a Kaduna, Maimuna Ahmed, Hauwa Shehu da Sa’adatu Abubakar.

KU KARANTA:Masu garkuwa da mutane sun yi gaba da daliban Jami’ar ABU 3 a hanyar Abuja-Kaduna (Hoto da Bidiyo)

Aisha wadda ta shigar da karar tana zama ne a Unguwar rimi dake Kaduna inda suke zaune gida daya tare da wadancan matan uku dake yi mata kazafin maita ita da mahaifiyarta.

“A gida daya muke zaune da su, haka kawai suka hadewa mahaifiyata kai gaba dayansu ban san me muka tare masu ba.” A cewarta.

Ta kuma roki kotu da ta shiga tsakaninsu da matan kana kuma bi masu hakkinsu da suka dauka nayi masu kazafin da ba su ji ba ba su gani ba.

Ana su bangaren kuwa wadanda ake tuhumar da aikata wannan laifin sun musanta zargin inda suka ce sam ba su aikata laifin ba.

Alkalin kotun, Malam Nasir Murtala bayan ya saurari tab akin bangarorin guda biyu sai ya nemi ko wannensu ya gabatar da shaidu a gaban kotun.

Haka kuma ya bada belin su a kan N50,000 ga ko wacce daya daga cikinsu sannan kuma ya daga shari’ar har zuwa 3 ga watan Satumba kamar yadda kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ya ruwaito.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel