Abin tausayi: Wani yaro mai shekari 13 ya farka ya ga dukkan mutanen gidansu sun mutu

Abin tausayi: Wani yaro mai shekari 13 ya farka ya ga dukkan mutanen gidansu sun mutu

Wani yaro mai shekaru 13 ya garzaya gidan makwabtansu neman taimako bayan ya farka ya ga dukkan mutanen gidansu sun mutu da sanyin safiyar ranar Lahadi.

Matashin, Sipho Miya, ya matukar dimauta bayan ya farka ya ga gawar kakarsa; Stella, mai shekaru 73, 'yar uwar mahaifiyarsa; Gugulethu, mai shekaru 35 da dan uwansa; Mpho Dube, mai shekaru 13, a gidansu da ke Sebokeng a kudancin birnin Johannesburg na kasar Afrika ta kudu.

Har yanzu ba tabbatar da mene ne takamaimai ya kashe mutanen gidan ba.

Kakakin rundunar 'yan sanda, Kaftin Teboho Lephoto, ya ce sun fara gudanar da bincike a kan musabbabin mutuwar mutanen.

Lephoto ya bayyana cewa rundunar 'yan sanda bata da tabbacin cewa mutanen sun mutu ne sakamakon shakar hayakin wani murhu da aka gani a gidan yana ci da wuta ko kuma sun ci guba ne a cikin abinci.

DUBA WANNAN: Soyayya: Saurayi ya maka budurwar da aka bashi a kotu bayan ta damfare shi miliyan N3

Wani makwabci da ya fara shiga gidan bayan Miya ya sanar da su ya bayyana cewa ya girgiza matuka bayan ganin gawar mutanen kwance a cikin gidan.

Kazalika, dangin mamatan sun bayyana cewar sun rasa me zasu ce dangane da mutuwar al'ajabin da 'yan uwansu suka yi.

Da wurin Stella, Mxolisi Miya, mai shekaru 53, ya bayyana cewa sun ji ciwon mutuwar mutane uku a danginsu lokaci guda.

"Mun ji ciwon mutuwarsu sosai ma kuwa, ban ma san me zan ce ba. Yayan mu ne ya kira mu ya sanar da mu cewa akwai bukatar mu zo Sebokeng saboda akwai matsala babba.

"Ba mu san cewa matsalar ta kai girman haka ba sai bayan da muka hango mutane sun cika kofar gidan a yayin da muke iso wa," a cewar Mxolisi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel