Mumunan hadari: Tirelan Dangote da doguwar motar haya sun yi kicibis

Mumunan hadari: Tirelan Dangote da doguwar motar haya sun yi kicibis

Wata tirelan Dangote dauke da Siminti ya samu mishkila a tsakiyar hanya kawai sai ya shigewa wata doguwar motar haya mai dauke da fasinjoji dake bakin hanya.

Direban motar na cikin halin ha'u'la'i kuma akalla fasinjoji goma sun jikkata kuma jami'an yan sanda sun garzaya da su asibiti.

Ganin abinda ya faru, direban tirelan ya gudu kuma ana nemansa ruwa a jallo.

A cewar hukumar kawo agaji na gaggawa ta jihar Legas LASEMA, an kokarin ceton rayukan wadanda abin ya shafa.

Mumunan hadari: Tirelan Dangote da doguwar motar haya sun yi kicibis
Mumunan hadari: Tirelan Dangote da doguwar motar haya sun yi kicibis
Asali: Facebook

KU KARANTA: Albishirinku: An fasa kara farashin wutar lantarki, NERC ta yi amai ta lashe

A jawabin suka ce: "Muna isa wajen, wata motar Dangote dauke da Siminti ta samu matsalar birki kawai tayi kicibis da doguwar motar hayar Primero mai lamba LSR-228XS dauke da fasinjoji 40 a zaune, 20 a tsaye."

"Dukkan fasinjojin da ke cikin motar sun samu rauni daban-daban amma mace daya ta rasa rayuwarta kuma direban na cikin halin ha'u'la'i saboda kafarsa ta dagargarje gaba daya."

"Gamayyar jami'an agaji tare yan sanda, FRSC, LASTMA suna aiki tukuru domin bude hanyar da kuma dauke motar."

A bangare guda, Hukumar yaki da fataucin muggan kwayoyi da haramtattun kayyakin a kasar Saudiyya ta yankewa akalla mutane 23 yan Najeriya haddin kisa.

An damke wadannan mutane 23 da tulin kwayoyi a cikinsu bayan sun hadiye. Hakan kuma ya sabawa dokokin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel