Na amince da shugaban ma'aikatan gwamnati na - Ganduje

Na amince da shugaban ma'aikatan gwamnati na - Ganduje

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya misalta shugaban ma'aikatan gwamnatinsa, Honarabul Ali Haruna Abubakar Makoda, a matsayin mutum nagari mai gaskiya da rikon amana kuma wanda ya fito daga gida na mutunci.

Ganduje ya ce Alhaji Makoda ya cancanci dukkanin wani yabo na mafi kololuwar karamci domin kuwa ya samu tabarraki a rayuwarsa ta kasance wa managarcin mutum wanda ya dabi'antu da gaskiya da rikon amana.

A yayin tuna baya gami da waiwaye wanda hausa ke cewa adon tafiya, gwamna Ganduje ya bayyana kyakkyawar alakarsa da mahaifin shugaban ma'aikatansa, Alhaji Bukar Makoda.

Ya ke cewa, "tsawon shekaru 30 da suka gabata mun yi aiki tare a ma'aikatar ayyuka, gidaje da kuma sufuri a lokacin mulkin soja, a yayin da Kanal Muhammad Abdullahi Wase ke rike da akalar jagorancin jihar Kano."

Wannan furuci ya fito daga bakin gwamna Ganduje a yayin da iyalan shugaban ma'aikatansa da kuma zuri'ar Alhaji Bukar Makoda suka ziyarci fadarsa da ke birnin Kanon Dabo, inda suka yi masa godiya ta bai wa dan uwansu amanar jagoranci.

A yayin murna gami da bayyana farin ciki da kuma annashuwa, gwamna Ganduje ya ce shi ne ya cancanci yi masu godiya a sakamakon sahalewa dan uwansu karbar nauyin jagoranci da gwamnatin sa ta rataya mai a wuyansa.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Jigawa ta ba da hutu ranar Talata

A wani rahoton na daban da jaridar Legit.ng ta ruwaito, wani masanin tattalin arziki na jami'ar jihar Kaduna, Dakta Aminu Usman, ya ce Najeriya ba zata taba taka mataki na ci gaba makamancin na kasar Indiya, Brazil ko kuma Chana a sanadiyar game ma'aikatar kudi da ta kasafi da tsaren-tsaren kasa da shugaban kasa Buhari ya yi a zango na biyu na gwamnatinsa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel