Labarin wani yaro mai suna Ali dan shekara 6 da yayi rayuwa cikin yan ta’addan Boko Haram

Labarin wani yaro mai suna Ali dan shekara 6 da yayi rayuwa cikin yan ta’addan Boko Haram

Wani yaro mai suna Ali ya bayyana halin da suka tsinci kansu tare da iyayensa bayan yan ta’addan Boko Haram sun kama su a garin Gwoza da ke jihar Borno.

Ali ya bayyana cewa yan ta’addan sun hallaka mahaifinsa a lokacin da yayi kokarin guduwa, yayinda su kuma suka dunga yi masu aikin bauta tare da yan uwansa da mahaifiyarsu.

Yace: “Yan ta’adda Boko Haram sun kama mu a lokacin da muke tserewa daga Ashigashia a Gwoza sannan suka dauke mu zuwa cikin daji. Mahaifina yayi kokarin tserewa amma suka harbe shi. Mahaifiyata, yan uwana da ni kaina mun yi zama tare da yan ta’addan.

“An bani aikin; ni ke wanke kayayyakinsu da goge takalmansu. Ana tashinmu da sassafe domin yin ayyuka. Duk wanda yaki yin aiki sai ayi masa mugun duka, na gan su da bindigoginsu da wasu irin makamai don haka kowa a tsorace yake.”

Ali dan shekara shida ne sannan a yanzu haka yana zama tare da mahaifiyarsa a wani sansanin yan gudun hijira da ke Maiduguri.

KU KARANTA KUMA: A na zargin Direbobi da laifin sace wasu karafuna a matatar Dangote

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoton a baya cewa Hukumar Kwastam na Najeriya a ranar Lahadi, 25 ga watan Agusta, ta bayyana cewa matocin yaki na sojoji da hukumomin Najeriya ta kama kwanan nan na jumhuriyar Nijar ne

Joseph Attah, kakakin hukumar Kwastam, ya bayyana cewa hukumomin Najeriya ta kuma damke direbobi shida da ke tuka motocin.

A kwanan nan ne rundunar sojin Najeriya a jihar Adamawa ta damke wasu manyan motocin yaki masu sile sannan ta mika su ga hukumar Kwastam a ranar Asabar.

An shigo da manyan motocin ne ba tare da takardun da suka kamata ba, ciki harda na mallakarsu, daga inda suka fito da kuma inda za su, lokacin da sojojin Najeriya suka kwace su a karamar hukumar Fufore.

Daga bisani sai aka damka su zuwa ga hukumar kwastam a wani taro da aka gudanar a Konkol, jihar Adamawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel