Hotuna: Gwamnoni 3 da suka tafi kasar Japan tare da Buhari

Hotuna: Gwamnoni 3 da suka tafi kasar Japan tare da Buhari

-Gwamnonin jihohin Borno, Kwara da Legas ne suka raka Shugaba Buhari zuwa kasar Japan

-Shugaban Najeriya zai halarci taron TICAD karo na 7 a Yokahama na kasar Japan wanda za ayi a ranakun 28 zuwa 30 ga Agusta

Shugaba Muhammadu Buhari ya bar Abuja a daren Lahadi zuwa kasar Japan inda zai halarci taron kasa da kasa domin cigaban Afirka karo na bakwai wato TICAD7. Taron zai gudana ne daga ranar 28 zuwa 30 ga watan Agusta a birnin Yokohama.

Hotuna: Gwamnoni 3 da suka tafi kasar Japan tare da Buhari
Hotuna: Gwamnoni 3 da suka tafi kasar Japan tare da Buhari
Asali: Facebook

Wannan shi ne karo na biyu kenan da Shugaba Buhari yake halartar irin wannan taron kasancewar ya halarci taron na 6 wato TICAD6 a Nairobi babban birnin Kenya a watan Agustan 2016.

Hotuna: Gwamnoni 3 da suka tafi kasar Japan tare da Buhari
Hotuna: Gwamnoni 3 da suka tafi kasar Japan tare da Buhari
Asali: Facebook

KU KARANTA:Abba Kyari: Fadar Shugaban Kasa ta ce babu abinda ya canja a ayyukansa

Bugu da kari, gwamnoni uku ne daga jihohin Najeriya suka yi rakiyar Shugaban kasa domin halartar wannan muhimmin taro. Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno, Abdulrahman Abdulrazaq na Kwara da kuma Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas.

Hotuna: Gwamnoni 3 da suka tafi kasar Japan tare da Buhari
Gwamnonin jihohin Kwara, Borno da Legas tare da Shugaba Buhari
Asali: Facebook

Haka zalika akwai wadansu ministoci a cikin tafiyar tare da manya-manyan jami’an gwamnati. Take taron na bana shi ne “Shirin Afirka da Yokohama na samar da cigaba mai daurewa”, a don haka Firai ministan Japan ne zai kasance babban mai masaukin baki da kuma yi jawabin barka da zuwa.

Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Femi Adesina ya ce shugaban Najeriya zai gabatar da jawabinsa ne a kan alakar Najeriya da Japan da kuma bitar abubuwan da aka tattauna wurin taron karon 6 wato TICAD6.

Bayan an kammala wannan taron ana sa ran Shugaba Buhari zai ziyarci fadar Sarkin Naruhito domin amsa gayyatar da yayi masa ta shan shayi a birinin Tokyo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel