Yanzu Yanzu: Sojoji sun kama motocin yaki guda 6 a Adamawa

Yanzu Yanzu: Sojoji sun kama motocin yaki guda 6 a Adamawa

Sojojin Najeriya da ke lura da wani wurin bincike a jihar Adamawa sun kama wasu motocin yaki guda shida da aka shigo da su Najeriya ba tare da bin tsari ba.

Jami’an sojojin Brigade 23 a Yola, sun kama kayayyakin a karamar hukumar Fufore a wannan makon.

Sai dai kuma ba ba san ko daga ina wadannan motoci suka tsallako Najeriya ba domin ba ma irin motocin sojojin Najeriya bane.

Koda dai hedkwatar rundunar sojin Najeriya tayi umurnin yin binciken gaggawa kan lamarin, an mika kayayyakin ga hukumar Kwastam na Najeriya.

Yanzu Yanzu: Sojoji sun kama motocin yaki guda 6 a Adamawa
Sojoji sun kama motocin yaki guda 6 a Adamawa
Asali: UGC

A ranar Asabar, kwamandan Brigade 23, S.G. Mohammed ya mika motocin ga kwanturolan Kwastam da ke kula da Adamawa da Taraba, Olumoh Kamaldeen, a wani taro da aka yi a Konkol, karamar hukumar Fufore.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kasar Saudiyya za ta hukunta yan Najeria 23 (jerin sunaye)

Sai dai babu bayani kan ko an kama wadanda ake zargi a yanzu. Haramun be shigo da irin wannan kaya ba tare da satifiket daga ofishin mai ba kasa shawara a harkar tsaro ba, wanda shine hukumar tarayya kadai da ke da wannan iko na bayar da irin wannan takarda.

Wannan lamari kuma na iya kara tunzura hukumomin tsaro, wadanda ke ci gaba da gwagwarmaya akan rashin tsaro da rikicin da ke faruwa a fadin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel