Ana zaton wuta a makera: Wurin saurayina na je, inji yarinya ‘yar shekara 14 da mahaifinta ke ikirarin saceta akayi

Ana zaton wuta a makera: Wurin saurayina na je, inji yarinya ‘yar shekara 14 da mahaifinta ke ikirarin saceta akayi

-Wata yarinya 'yar sakandare ta tayar da hankalin mahaifinta yayin da ta ziyarci saurayinta a wani gari

-Mahaifin yarinyar ya gaggawar kai rahoto ofishin 'yan sanda inda yake tunanin cewa an sace diyar tasa ne

-Yarinyar da bakinta ta fadi cewa wurin saurayinta ta je babu kuma wanda ya saceta

Wata yarinya ‘yar aji uku a matakin karamar sakandare wato JSS 3 mai shekaru 14 a duniya ta shaidawa ‘yan sanda cewa ita fa ba saceta akayi ba ta wurin saurayinta ne.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, SP Ebere Amaraizu ne ya fitar da wannan labara a ranar Asabar.

KU KARANTA:Zamu tsamo ‘yan Najeriya miliyan 50 daga talauci – Pantami

Mista Frank Anioma mahaifin yarinyar shi ne ya garzaya ofishin ‘yan sanda da batun cewa an sace masa yarinyarsa mai suna Kosisochukwu Anioma.

A cewar kakakin ‘yan sandan, “ Anioma ya fara yada labarin satar diyar tasa ne a shafukan sada zumunta. Kana daga bisani ya kai rahoto wurin ‘yan sanda.

“ A ranar 22 ga watan Agusta muka samu wannan labari na cewa an sace diyar Anioma, ba tare da bata lokaci ba jami’anmu suka bazama zuwa ga neman wannan yarinya.”

Kakakin ya cigaba da cewa, abinda suka samu dangane da wannan labarin ya sha bamban da labarin da mahaifinta yake yadawa.

Da take magana a kan wannan batu, yarinyar ta ce ba saceta akayi ba da kafarta ta je Owerri domin kai wa saurayinta ziyara saboda sun dade ba su hadu ba.

Kamar yadda ta fadi a cikin kalamanta, Kosisochukwu ta shaidawa ‘yan sanda cewa saurayin nata ajinsu daya a makarantarsu dake Abakiliki. Don haka ta zabi ta kai masa ziyara ne bayan an ba su hutu mai tsawo a dalilin haka sun jima ba tare da sun ga juna ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel