An yanka ta tashi: ‘Yan sanda sun ji shiru bayan watanni 10 da yi masu karin albashi

An yanka ta tashi: ‘Yan sanda sun ji shiru bayan watanni 10 da yi masu karin albashi

Kimanin watanni goma kenan da Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan karin albashi jami’an ‘yan sandan Najeriya sai dai har yanzu jami’an basu soma amfana da sabon albashin ba.

A wani binciken da jaridar The Punch ta gudanar ya kawo mana cewa jami’an ‘yan sandan har yanzu dai ana biyansu ne tsohon albashi kamar yadda aka saba.

KU KARANTA:Mafi karancin albashi: Gwamnatin tarayya za ta gana da kungiyar ‘yan kwadago

Shugaban kasa ya rattaba hannu a kan karin albashin tun watan Nuwamban 2018 wanda zai habbaka albashin jami’an hukumar ‘yan sandan.

Wannan rattaba hannun na Shugaban kasa na nufin cewa albashin jami’an ‘yan sanda zai karu a ko wane mataki wanda ya hada da alawus da kuma fansho.

Amma sai dai wasu kanana da manyan jami’an ‘yan sandan da suka zanta da manema labarai ranar Alhamis a Abuja sun ce maganar karin albashin “ba komi ba ce illa labarin kanzon kurege.”

Da yake magana da ‘yan jarida a kan wannan al’amari wani jami’in ASP wanda yake aiki a garin Abuja ya ce, rashin fara biyan sabon albashin ya tabbatar da cewa gwamnati ba ta damu jin dadi da walwalar ‘yan sanda ba.

ASP ya ce: “ A lokacin da muka samu labarin karin albashin munyi matukar murna kwarai da gaske. Amma sai dai kash babu abinda muka gani har yanzu sai bacin rai kawai.

“ Da ace wannan karin ya shafi ‘yan siyasa ne da tuni an manta da kaddamar da shi. Rashin biyan wannan sabon albashin gaba daya ya sace mana gwiwa.”

Haka zalika wani Kwamishinan ‘yan sandan da ya nemi a boye sunansa ya soki gwamnati a kan rashin kaddamar da karin albashin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel