Mamakon ruwan sama ya yi awon gaba da kananan yara 3 a jahar Kano

Mamakon ruwan sama ya yi awon gaba da kananan yara 3 a jahar Kano

Wani ruwan sama kamar da bakin kwarya daya sauka a ranar Laraba, 21 ga watan Agusta a jahar Kano ya yi sanadiyyar mutuwar wasu kananan yara guda uku a unguwar Saidawa dake cikin karamar hukumar Danbatta.

Rahoton jaridar Punch ta bayyana jami’in watsa labaru na karamar hukumar Danbatta, Nura Umar ya bayyana cewa yara uku da suka hada da mata biyu da namiji daya sun mutu ne biyo bayan ambaliyan ruwan sama da aka samu a sanadiyyar ruwan sama.

KU KARANTA: Yaba kyauta tukwici: Sarkin Zaria ya baiwa Buhari kyautar ingarman doki

Malam Nura ya bayyana cewa ambaliyan ruwan ya shafi yankunan Fagwalawa, Makera, Turu da unguwar Mahuta, kuma ya lalata dimbin dukiyoyi, kadarori da gonakai, inji rahoton majiyar Legit.ng.

Mukaddashin shugaban karamar hukumar Danbatta, Musa Danbatta ya kai ziyarar jajantawa ga jama’an da ibtila’in ya shafa, inda ya mika musu kayan tallafi, sa’annan ya yi addu’an Allah Ya jikan mamatan, tare da fatan Allah ya baiwa iyayensu hakurin rashi.

A wani labarin kuma, Ajali da ke zuwa ba tare da an ankara ba, ya cimma wani yaro mai shekaru 12, Sama'ila Safiyanu, yayin da ya nutse yana tsaka da wankar rafi cikin wani gulbi a unguwar Sharada Kwanar Mai jego da ke birnin Kanon Dabo.

Kakakin hukumar kwana-kwana na jihar Kano, Alhaji Sa'idu Muhammad, shi ne ya bayar da shaidar wannan mummunan rahoton yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, inda yace mummunan tsautsayin ya auku da sanyin safiyar ranar Alhamis, yayin da mamacin ya fita wankan rafi.

Jami'an hukumar kwana-kwana sun tsamo gawar marigayi Sama'ila a rafin da ke unguwar Sharada, inda aka mika ta ofishin 'yan sanda na kurkusa inji Alhaji Sa'idu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel