Ba zan lamunci rashin da’a ba, ministan noma ya yi gargadi

Ba zan lamunci rashin da’a ba, ministan noma ya yi gargadi

Ministan noma da raya karkara, Sabo Nanono, ya yi gargadin cewa ba zai lamunci rashin da a da yiwa aiki rikon sakainar kashi ba a matsayinsa na minista.

Yayinda yake umurtan dukkan ma’aikata akan su tsaya tsayin daka wajen aiki, yace “na yi aiki a hukumomin gwamnati da masu zaman kansu, sannan na san yadda mutane ke aiki a hukumomin biyu”.

Ya fada ma manema labarai cewa zai taba kowa wajen gudanar da hakkokin da suka rataya a wuyansa bayan rantsar dashi a fadar shugaban kasa a ranar Laraba, 21 ga watan Agusta.

Ya kuma bayyana cewa zai tabbatar da cewa harkar noma ya dawo da martabarsa saboda ya shiga cikin wani hali sakamakon tsaron cikin gida.

Ya bayyana cewa ma’aikatar noma na daya daga cikin ma’aikatun kasar da ke cikin wani hali, sannan cewa ba ta kulawar da ya kamata zai taimaka wajen magance matsaloli da dama.

KU KARANTA KUMA: Ngige, Malami da sauran ministoci 10 da zasu maimaita mukamansu a zango na biyu

Ya bukaci sassa da ke da nasaba akan su kammala aiki kan kasafin kudin domin cimma wa’adin watan Satumba da majalisar dokokin tarayya ta bayar na karban kasafin kudin domin ta samu daman kammala aiki akai zuwa watan Oktoba.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa ministan zai yi rangaji a hukumomi 40 da ke karkashin ma’aikatar domin sanin ayyukansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel