Zaben Shugaban kasa a 2023: Ku tsayar dan takara daga Arewa, wani tsohon dan majalisa yayi kira ga jam’iyyun siyasa

Zaben Shugaban kasa a 2023: Ku tsayar dan takara daga Arewa, wani tsohon dan majalisa yayi kira ga jam’iyyun siyasa

Wani tsohon dan majalisar dattawa Sanata Roland S. Owie ya roki jam’iyyun siyasa kan cewa su tsayar da dan takarar shugabancin kasa daga Arewa a zaben shekarar 2023 wanda ke tafe nan gaba.

Sanata Owie ya bada wannan shawarar ne a ranar Talata a wani zance da ya fitar inda yake martani game da ce-ce kucen da wasu manyan mutane daga yankunan Kudu da kuma Arewacin kasar nan ke yi a shafukan sadarwa.

KU KARANTA:Kaduna: Al’ummar jihar na yabawa El-Rufai a kan irin ayyukan da yake yi na cigaba

Ga abinda ya fadi a cikin zancen na sa: “ Na ci karo da wani zancen da ya ja hankalina a shafi na 6 cikin jaridar The Sun ta ranar Litinin 19 ga watan Agusta a kan wata muhawara da wasu manyan mutane uku suka tafka a kan shugabancin kasa a 2023.

“Wadannan mutanen kuwa su ne, Cif Ayo Adebanjo, surukina Cif Chukwuemeka Ezeife da kuma Ambasada Yahaya Kwande. Sam ban taba tunanin manyan mutane za su iya yin muhawara game da abinda aka riga aka samu yarjejeniya a kansa tun shekarar 1999.

“ A shekarar 1999, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wanda ya fito daga Kudu ya shekara takwas a bisa mulki. Bayan ya sauka sai ya mika mulki zuwa ga hannun dan Arewa wato Umaru ‘Yar’Adua.

“ ‘Yar’Adua bai kammala ko wa’adinsa na farko Allah yayi masa cikawa, mulki ya sake dawowa kudanci. A don haka idan kukayi lissafin daga shekarar 1999 zuwa yanzu dimokuradiyya na da shekaru 20 a Najeriya. Kudanci sun samu shekara 13 suna mulki.

“ Wannan dalilin ne ya sa nake ganin cewa arewa nada ragowar shekara bakwai domin cikin wa’adinta kafin mulki ya sake dawo kudanci.” A cewarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel