Duba kaga sabbin kwamishonin Jihar Legas su 21 (Sunaye)

Duba kaga sabbin kwamishonin Jihar Legas su 21 (Sunaye)

Ga jerin sunayen sabbin kwamishinonin Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas kamar yadda jaridar The Nation ta fitar da su:

1. Rabiu Olowo Onoalapo – Kwamishinan kudi

Rabiu yayi aiki a wurare da dama inda yak ware a fannin kididdigar kudi. Ya kuma samu wata lambar yabo daga kungiyar AFCE ta Yammacin Afirka.

2. Misis Folashade Adefisayo –Kwamishinan ilimi

Folashade ta kware sosai a fannin ilimi inda ta ked a kwarewar aiki ta sama da shekaru 20. Haka zalika it ace shugaban Leading Learning Limited wanda ta kafa a shekarar 2014.

KU KARANTA:An kama gawurtaccen mai garkuwa da mutane nan Wadume a Taraba

3. Farfesa Akin Abayomi – Kwamishinan lafiya

Aboyomi kwararren likita ne wanda ya shahara a kan bangaren tsaftar muhalli. Yayi karatunsa na likitanci a kasar Ingila wato Royal Medical College dake Landan.

4. Dr Idris Salako – Kwamishinan tsarare da cigaban birane

Idris shi ne shugaban Adesanya Salako and Associates. Har wa yau, daya daga cikin mambobin kungiyar masu fitar da taswirar biranen Najeriya ne, wato NITP.

5. Tunji Bello – Kwamishinan ruwa da muhalli

Bello yayi aiki a wurare da dama ciki hadda First Bank of Nigeria. Tunji Bello ya rike mukamin sakataren gwamnatin jihar Legas a gwamnatin da ta gabata.

6. Gbenga Omotoso – Kwamishinan yada labara

Gbenga kwararren dan jarida ne wanda ya taba lashe kyauta tare da The Nation Newspaper a matsayin edita.

7. Misis Bolaji Dada – Kwamishinan lamuran mata da kawar da talauci

Dada ta taba zama mataimakiyar shugaban karamar hukumar Apapa har sau biyu. Ta kuma yi karatun digirinta na farko a Jami’ar Jihar Legas inda ta kammala a shekarar 1991.

8. Lere Odusote – Kwamishinan lantarki da ma’adanan kasa

9. Dr Federic Oladeine – Kwamishinan sufuri

10. Gbolahan Lawal – Kwamishinan noma

11. Moruf Akinderu Fatai – Kwamishinan gidaje

12. Moyo Akinderu Fatai – Kwamishinan shari’a

13. Hakeem Fahm – Kwamishinan kimiyya da fasaha

14. Misis Ajibola Ponnle – Kwamishinan kaddamarwa da fansho

15. Engr. Aramide Adeyoye – Kwamishinan ayyuka

16. Segun Dawodu – Kwamishinan wasanni da cigaban matasa

17. Misis Uzamat Akinbile Yusuf – Kwamishinan harkokin cikin gida

18. Misis Yetunde Arobieke – Kwamishinan kananan hukumomi

19. Misis Lola Akande – Kwamishinan kasuwanci

20. Misis Olufunke Adebolu – Kwamishinan al’adu da harkokin bude ido

21. Sam Egube – Kwamishinan kasafi da tattalin arziki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel