Bankin Duniya ya tona yadda wasu kamfanonin China 6 ke cin karensu ba babbaka a Najeriya
Rahotanni da ke zuwa mana ya nuna cewa Babban Bankin Duniya ya tona sunayen wasu manyan kamfanonin gine-gine na kasar China har guda shida, akan cewa an same su da laifin harkallar kwangiloli masu tarin yawa.
Bankin yace wadannan kamfanoni da ke gudanar da aiki a wurare daban-daban a fadin Najeriya, sun karya ka’idojin ayyukan kwangilolin da bankin duniya ya gindaya a fadin duniya. Kuma bankin ya nuna rashin jin dadin sa.
Wadannan kamfanoni dai sun hada da:
1. China Railway Construction (International) Nigeria Company Limited.
2. China Railway 18th Bureau Nigeria Ltd.
3. China Nageria Engineering Company Ltd.
4. CCECC Nigeria Lekki (FTA) Construction Ltd.
5. CCECC Railway Petroleum and Gas Company Ltd.
6. CCECC Nigeria Company Ltd.
A yanzu dai wadannan kamfanoni ne ke cin karensu ba bbaka aNajeriya su na ayyukan kwangilolin gina hanyoyin jiragen kasa, titinan gwamnatin tarayya da na jihohi, gina rukunin gidaje na gwamnatin tarayya da gwamnatin jihohi, gina filayen saukar jirage da ma harkokin man fetur da wasun su ke yi.
Bankin Duniya ya haramta su daga cikin kamfanonin da ya amince a bai wa duk wata kwangilar da ta shafi harkar kudaden da aka ramto ne daga Bankin Duniya ko kwangilar bankin, har tsawon shekara daya. Wato daga Yunin 2019 zuwa Yulin 2020, 3 Ga wata.
Bankin Duniya ya ce wadannan kamfanoni sun rika karya ka’idojin da bankin ya shimfida wajen gudanar da kwangiloli ba tare da nuku-nuku ba, ko harkalla ko rufa-rufa ba.
Bankin ya ce an rika gudanar da wasu kwangilolin ba tare da cikakken bayanin yadda aka kashe kudaden da hujjar abin da aka yi da kudaden ba.
Takardar nuna bacin rai da Bankin Duniya ya fitar a cikin shafin sa na Intanet duk ya bayyana wannan bayani.
KU KARANA KUMA: Umurnin kwace kadarorin Najeriya a Birtaniya: Gwamnatin Buhari na shirin kama wasu jami’ai da ke da hannu a hukuncin
Sai dai kuma bai fayyace dalla-dalla adadin kudaden da kamfanonin suka yi wa babakere ba. Amma dai ya ce sun karya ka’idar dokar da bankin ya shimfida ta 1.16(a)(ii).
Kamfanin China Railways dai shi ne ke aikin titin jirgin kasar nan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna. Ya na daga cikin katafariyar kwangilar dala bilyan 18, wato kwatankwacin naira tiriliyan 2 na aikin kwangilolin hanyoyin jirgin kasa a fadin kasar nan.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng