Yanzu Yanzu: Gobara ta tashi a sananiyyar kasuwar Katangowa da ke Lagas (hotuna)

Yanzu Yanzu: Gobara ta tashi a sananiyyar kasuwar Katangowa da ke Lagas (hotuna)

Rahotanni sun kawo cewa gobara ta tashi a sananiyyar kasuwar nan na siyar da kayan gwanjo wanda aka fi sani da Katangowa da ke Lagas, inda ta lakume shagunan da ke kallon babban masallacin Juma’a a kasuwar.

Kasuwar na a yankin karamar hukumar Agbado/Okeodo, hanyar babban titin Lagos-Abeokuta.

Legit.ng ta tattaro cewa mazauna yankin sun ce gobarar ta fara ne da misalin karfe 3:00 na tsakar dare, inda ta lalata shaguna da kayayyakin gwanjo.

Yanzu Yanzu: Gobara ta tashi a sananiyyar kasuwar Katangowa da ke Lagas (hotuna)
Yanzu Yanzu: Gobara ta tashi a sananiyyar kasuwar Katangowa da ke Lagas
Asali: UGC

A cewar rahoto, an tura jami’an hukumar kashe gobara da na hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Lagas domin su kashe gobarar.

Yanzu Yanzu: Gobara ta tashi a sananiyyar kasuwar Katangowa da ke Lagas (hotuna)
Gobara ta tashi a sananiyyar kasuwar Katangowa da ke Lagas
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Fadar Shugaban kasa ta caccaki rahoton Financial Times akan jawabin Buhari na shigo da abinci

Hakazalika jami’an yan sanda daga hedkwatar Oke Odon a wajen, domin hana sace-sace a shagunan da gobarar bai kai ba.

A wani labarin kuma mun ji cewa, Hukumar yan sandan jihar Legas ta damke mutane biyar tattare da rikicin da ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a kasuwar Oke-Ado dake jihar Legas.

Jami'in hukumar, DSP Bala Elkana, ya bayyana ainihin abinda ya sabbaba wannan rikici da kuma matakin da jami'an yan sanda suka dauka domin kwantar da kuran kafin ya kai ga asarar rayuka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel