Soja mazan fama: Sojojin Najeriya su ne na 4 a jerin sojojin Afirka mafiya karfi

Soja mazan fama: Sojojin Najeriya su ne na 4 a jerin sojojin Afirka mafiya karfi

-Sojojin Najeriya sune na 44 a jerin sojojin da suka fi karfi a duniya

-A nahiyar Afirka kuwa Najeriya ce a mataki na hudu bayan kasashen Masar, Aljeriya da kuma Afirka ta Kudu

Rundunar sojin Najeriya ta zo a mataki na hudu a fadin Nahiyar Afirka a cikin wannan shekarar ta 2019 a jerin kasashen mafiya karfin soji.

A bisa binciken Globalfirepower, sojin Najeriya sun samu maki 0.7007 na Power Index. Hakan ne ya ba su damar zuwa a mataki na hudu bayan kasashen Masar, Aljeriya da Afirka ta Kudu wadanda suke kan gaba a Nahiyar Afirka.

KU KARANTA:Falana ya gargadi gwamnatin tarayya a kan rashin lafiyar Zakzaky da matarsa

Bugu da kari, a matakin duniya kuwa Najeriya ta na mataki na 44 ne kamar yadda Globalfirepower ta wallafa a shafin yanar gizo.

Majiyar Legit.ng ta tattaro mana bayanin cewa a bara ma irin wannan matakin sojin Najeriya su ka samu sai ga shi kuma a bana sun cigaba da rikon matsayin nasu.

Kasar Masar a nahiyar Afirka ita ce ke matakin na daya, yayin da a jerin kasashen duniya kuwa ta ke a mataki na 12 da maki 0.2283 na Power Index.

Mai bima kasar Masar a nahiyar Afirka ita ce kasar Aljeriya inda kuwa a jerin kasashen duniya take a mataki na 27 da maki 0.4551.

Kasar Afirka ta Kudu ita ce a mataki na uku yayin da a jerin kasashen duniya take a mataki na 32 da maki 0.5405.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel