Ga irinta nan ai: Daga zuwa iskanci da saurayi a Otel ya shaketa har lahira, bayan ya gama zina da ita

Ga irinta nan ai: Daga zuwa iskanci da saurayi a Otel ya shaketa har lahira, bayan ya gama zina da ita

- Mako biyu kawai bayan iske wata budurwa da aka kashe a wani otel dake birnin Fatakwal a jihar Rivers

- Ranar Larabar nan da ta gabata an sake iske wata budurwar dai a wani Otel daban, inda ita ma aka shaketa har lahira

- Jami'an hukumar 'yan sanda dai sun bayyana cewa sun cafke wasu da ake tunanin suna da hannu a kisan yarinyar

An sake samun gawar wata budurwa an kashe ta har lahira ta hanyar shaketa da tsumma a wani Otel dake birnin Fatakwal, mako biyu da suka gabata an iske gawar wata budurwa ita ma da hakan ya faru da ita.

Lamarin ya faru ranar 13 ga watan Agusta kamar yadda rundunar 'yan sandan jihar Rivers ta bayyana, daga bakin kakakin rundunar, Nnamdi Omoni.

Da yake magana akan kisan budurwar, wakilin gidan rediyon Cool FM, Nnamdi Onwuka ya bayyana cewa an gano sunan yarinyar da aka kashe din Jennifer. Ya kuma gargadi 'yan mata da su dinga sanin irin mutanen da suke mu'amala dasu.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Tun farko Buhari bai cancanci tsayawa takara ba - Atiku Abubakar

Ga abinda Onwuka ya ce:

"Ina ganin akwai mutumin da yake kashe 'yammata a cikin birnin Fatakwal. An kara samun gawar wata budurwar an kasheta a wani Otel jiya. Mako biyu kawai bayan an gano gawar wata budurwa da ita ma irin wannan lamarin ya faru da ita.

"Dan Allah 'yammata ku dinga lura da mutanen da kuke mu'amala da su, saboda kada irin haka ta cigaba da faruwa.

"Yanzun nan na fito daga cikin otel din da lamarin ya faru, kawar budurwar ta bayyana cewa sunanta Jennifer."

Jami'an hukumar 'yan sanda sun bayyana cewa an kama wasu da ake tunanin suna da hannu a wannan lamari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel