Hajjin bana: Masari yayi kyautar kudi ga mahajjatan Katsina su 3,086

Hajjin bana: Masari yayi kyautar kudi ga mahajjatan Katsina su 3,086

-Aminu Masari ya ba alhazawa Jihar Katsina kyautar N30,000 ga ko wannensu

-Amirul hajjin jihar na bana Muntari Lawal ne ya fitar da wannan labarin ranar Juma'a a Makkah yayin da yake hira da 'yan jarida

-Muntari ya sanar a cikin jawabinsa cewa sun kammala tsare-tsaren soma jigilar alhazawan zuwa Najeriya

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bada kyautar riyal 300 ga mahajjatan jihar Katsina su 3,086 dake kasar Saudiya a halin yanzu. Riyal 300 daidai yake da N30,000 kudin Najeriya.

Amirul hajjin jihar Katsina, Alhaji Muntari Lawal ne ya bada sanarwar wannan labarin ranar Juma’a a birin Makkah lokacin da yake hira da manema labarai.

KU KARANTA:Kotu ta kulle asusun bankin tsohon gwamnan Zamfara

Ya ce kyautar kudin ta na matsayin gudunmuwace ga mahajjata da suke na farko a sahun tafiya Saudiya domin sauke faralin aikin hajjin bana.

Lawal ya kara da cewa, wannan gudunmuwar ta fara ne tun a lokacin gwamnatin da ta shude a Jihar Katsina saboda ya kasance babu wani mahajjacin da ya shiga matsalar rashin guzuri a Saudiya.

Bugu da kari, ya yabawa mahajjatan jihar bisa yadda suka gudanar da aikin hajjin nasu cikin tsanaki, inda ya kara da kira a garesu cewa su dore a kan abinda suka gudanar na ibada a kasa mai tsarki bayan dawowa Najeriya.

Amirul hajjin ya shaidawa manema labarai cewa sun kammala tsare-tsaren fara jigilar mahajjatan domin dawowa Najeriya.

Daya daga cikin mahajjatan da suka samu wannan kyautar, Hajiya Safiya Daura ta yabawa gwamnati saboda wannan kyautar kudi inda ta ce, kyautar za ta taimkawa alhazawa musamman wadanda suke son yin tsaraba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel