Dan shekara 16 ya zama Kakakin Majalisar Yara a Jihar Katsina

Dan shekara 16 ya zama Kakakin Majalisar Yara a Jihar Katsina

-Ibrahim Maharazu ya zama Kakakin majalisar yara a jihar Katsina

-Maharazu mai shekaru 16 ya samu nasarar hawa wannan kujerar ne bayan ya doke abokiyar takararsa da kuri'a 27 yayin da take da 6 kacal

-Jamila Lawal ita aka zaba a matsayin mataimakiyar kakakin majalisar ta yara

Ibrahim Maharazu mai shekaru 16 wanda ya fito daga makarantar Family Support School, Daura ya samu nasarar zama Kakakin Majalisar Yara ta Katsina a ranar Alhamis 8 ga watan Agusta.

Maharazu dai ya samu nasarar hawa wannan kujerar ne da kuri’a 27, bayan da doke abokiyar takararsa Aisha Nakano wadda ta samu kuri’a 6 kacal. Zango mulkinsa shekara uku ne.

KU KARANTA:Kisan ‘Yan sanda: Sojoji da ‘yan sanda sun kafa kwamitin bincike na hadin gwiwa

Ita dai wannan majalisa ta yara na samun goyon baya ne daga Save the Children International wato SCI wadda ke ba yaran damar fadin kokensu game da hakkin da ya shafi ‘yancinsu.

Da yake magana jim kadan bayan ya kammala rantsuwar kama aiki, Maharazu ya dau alkawarin kiyaye ‘yancin yara a jihar Katsina da kuma wasu matsalolin da suka dangancensu.

Ya kuma yi kira ga sauran mambobin majalisar da su ba shi goyon bayan domin cinma abinda ya sa gaba. Manufarsa da ita ya zamana an tsare ‘yancin yaran dake jihar Katsina, a cewar Kakakin.

Sauran zababbun ‘yan majalisar sun hada da, Jamila Lawal (Mataimakiyar Kakaki), Aisha Nakano ( Shugabar Majalisa), Maryam Muktar ( Mataimakiyar Shugaban majalisa), Aliyu Nasir ( Shugaban masu rinjaye), Saddiq Badamasi ( Magatakardan majalisa) da kuma Rabi’u Babangida ( Sajan).

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel