Tashin hankali: Yarinya ‘yar shekara 5 ta bata daga zuwa sayen biskit

Tashin hankali: Yarinya ‘yar shekara 5 ta bata daga zuwa sayen biskit

-Wata yarinya 'yar shekara biyar da haihuwa ta bata a Legas

-Mahaifin yarinyar ya shaidawa manema labarai cewa tun ranar 19 ga watan Yuli yarinyar ta bata a daidai lokacin da ta bar gida domin zuwa wurin sayen biskit

-Maihifin yarinyar mai suna Ramon Murtala ya shaidawa manema labarai cewa tuni suka kai rahoton batar yarinyar ofishin 'yan sanda

Wata yarinya mai suna Zainab Murtala, ‘yar shekara biyar da haihuwa ta yi sama ko kasa tun ranar 19 ga watan Yuli da ta tafi wurin sayen biskit.

Ita dai wannan yarinyar tana zaune ne tare da gwaggonta a gida mai lamba 1B Abikoye Street, Amukoko jihar Legas.

KU KARANTA:Babbar magana: El-Zakzaky baida bambanci da Shekau, inji Yayansa

Ramon Murtala wanda shi ne mahaifin yarinyar ya shaidawa jaridar The Nation cewa Zainab ta bata ne da misalin karfe 7 na yammacin 19 ga watan Yuli bayan da ta tafi wurin sayen biskit.

Da yake bada karin bayani a kan lamarin, Murtala ya ce: “ Ta kasance tana wasa ne a kofar gida da misalin karfe bakwai na yammancin 19 ga watan Yuli, daga bisani kuma ta shiga gida inda ta karbi kudi wurin kanwata domin ta sayi biskit. Tunda ta yi wannan fitar da nufin zuwa wurin sayen biskit ba mu sake ganinta ba har yanzu.

“ Mun kai rahoton batar wannan yarinyar zuwa ofishin ‘yan sanda amma babu wani labarinta har ila yau.” Inji Murtala.

A karshe ya kara da rokon jama’a cewa duka wanda ya samu labarin ganin yarinyar da ya garzaya ofishin ‘yan sanda mafi kusa domin kai rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel