Babbar magana: El-Zakzaky baida bambanci da Shekau, inji Yayansa

Babbar magana: El-Zakzaky baida bambanci da Shekau, inji Yayansa

-Babban yayan Ibrahim El-Zakzaky ya ce kungiyar shi'a ba ta da bambanci da boko haram

-Sheikh Muhammad Sani Yakub shi ne ya fadi wannan maganar a wata zantawa da yayi da manema labarai a Zariya

-A cewar Muhammad Sani abinda gwamnati tayi yayi daidai bisa haramta ayyukan shi'a da tayi a Najeriya

Yaya a wurin Shugaban kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) wadda aka fi sani da Shi’a, Sheikh Muhammad Sani Yakub yayi fashin baki a kan haramta ayyukan shi’a inda ya ke cewa hakan ya yi daidai.

Sheikh Muhammad Sani wanda yake babban wa ga Ibrahim El-Zakzaky shi ne Shugaban Kungiyar Izala ta Zariya. Kuma ya furta wannan maganar tasa ne a wata hira ta musamman da yayi da manema labarai a Zariya.

KU KARANTA:Babu dan Najeriyar da zai yi da na sanin sake zabar Buhari – Omo-Agege

A cewarsa ba haramta ayyukan shi’an kawai ya kamata gwamnati tayi ba, gaba daya ya kamata a ce an kori kungiyar daga Najeriya.

Haka zalika, ya kara da cewa wannan kungiya ta shi’a bata da wani bambanci da kungiyar Boko haram, inda ya ce kaninsa El-Zakzaky bai da bambanci da Shekau.

Sheikh Muhammad Sani ya ce: “ Kamar yadda kuka sa ni dai El-Zakzaky dan-uwana ne na jini, mahaifinmu daya da shi. A lokacin da muka taso bani da abokin da ya wuce shi kafin ya fara shi’a kenan. Komai namu tare muke yi hatta makaranta ma daya muke zuwa ta islamiya.

“ Mun yita ja masa kunne a kan wannan bakar akida amma ya ki ji. A gani na tun da dadewa ya kamata a ce gwamnati ta sallami al’amuran wannan kungiyar saboda babu wani abu mai kyau a tare da kungiyar shi’a.

“ Wai shin in tambayeku mana, a duk fadin duniyar nan ina kuka taba ganin an rufewa Hafsun sojoji hanya? Amma a kasar nan ‘yan shi’a sunyi hakan, sai yanzu gwamnati ta ga cewa ya kamata ta haramta ayyukansu. Babu wani laifi da gwamnati tayi abinda akayi ya dace dari bisa dari.” Inji yayan Zakzaky.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel