Abubuwa 10 da bai kamata miji ya fada wa matarsa ba

Abubuwa 10 da bai kamata miji ya fada wa matarsa ba

Masu iya magana dai na cewa ‘ Magana zarar bunu ce’, a don haka duk kalaman da mutum zai furta kan iya zama sanadiyar gyara ko wargaza zamantakewarsa da iyalinsa.

Ga jerin wasu abubuwa goma da ya kamata duk wani miji ya guji furtasu ga matarsa, saboda mata dan karamin abu kan iya sanya su cikin damuwa:

1. Ya rage naki

Mafi yawan mata basu son jin wannan Kalmar. A wasu lokutan zai kasance kana hasashen yin wani abu sai matarka ta baka shawara ko dai kaza zamu yi ne, fadin ya rage naki na matukar bata wa mata rai.

KU KARANTA:Wasu matasa uku sun gurfana gaban kotun ta'amuni da tabar wiwi

2. Ban iya tuna lokacin da na fadi hakan

Haba yallabai, ya zaka fadi magana kuma kace ka mance lokacin da ka fade ta. Yana da kyau mu tuna mata na da kokarin rike abu a kwakwalwarsu, fadin wannan kalamin kan iya haddasa fitina tsakanin mata da miji.

3. Ban sani ba

Wasu lokutan ma tambaya kadan mata za tayi wa mijinta, kawai amsar da zai furta mata ita ce ‘ban sani ba’. A rika tauna magana kan a fade ta domin gyaran zaman takewa.

4. Ba komai

Wasu mazan na da dabi’ar yin biris da matansu, da kuma matar ta tambaya ko lafiya sai ka ji sun ce ba komai.

5. Zanyi amma ba yanzu ba

Ba yanzu ba, to sai yaushe? Ba yanzu ba kan iya daukar tsawon lokaci marasa adadi. Ina laifin ka sa lokaci kamar mako guda ko wata guda haka.

6. Meye kikeyi tun safe

Wannan kalamin na bakanta ran mata, miji zai fita wurin aiki ya bar mace da dawainiyar yara sai kaji ya dawo abu kadan sai ya fara fadin meye kikeyi tun wayewar gari.

7. Bace min daga gani

Idan rai ya baci hankali ke nemo shi, don kun samu rashin jituwa da matarka bai kamata ka furta mata wannan kalma ba wadda aka tsari da tsawa ake yenta.

8. Kin fiye yin…. ko baki taba yin abu kaza ba

Korafi baida dadi musamman ga mace. Ai maimakon ka zauna kana kusheta mai zai hana kayi amfani da dubara cikin zance sai ka sako matsala daya ba tare da ka bata mata rai ba.

9. Ai duk laifinki ne

Ko da kuwa laifin nata ne da gaske, kamata yayi ka samu wata hanyar lurar da ita domin ta gyara ko dan gaba.

10. Kin fiye kiba

Ka guji furta duk wata Kalmar da ka san za ta bata ran matarka. Ko da kuwa tana da kibar ai ba abinda ya kamata ka rika hantarar ta bane a kai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel