Wani jirgin sojoji ya rikito bisa gidajen mutane a Pakistan
-Wani jirgin saman sojojin Pakistan yayi hatsari a wata unguwa dake kusa da birnin da hedikwatar sojin kasar take
-Mutane 18 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon hatsarin jirgin da ya fada bisa wani gida yana ci da wuta
-Wani ganau ya bayyana mana cewa tun jirgin na sama ya fara ci da wuta
A kalla mutum 18 ne suka rigamu gidan gaskiya, yayin da wasu da dama suka jikkata a sakamakon hatsarin wani karamin jirgin soji da ya fado a wata unguwa dake kusa da birnin Rawalpindi na Pakistan.
Mutum biyar dake cikin jirgin da kuma fararen hula 13 na daga cikin wadanda suka mutu a sanadiyar hatsari kamar yadda hukumar agaji ta bada labari.
KU KARANTA:Da zafinsa: Kotun Koli ta tsige dan majalisar APC
Hatsarin ya faru ne a daidai lokacin da jirgin ke gudanar da atisaye. Wani wanda lamarin ya auku a kan idonsa ya bamu labarin cewa tun jirgin na sama kan ya fado ya soma ci da wuta.
Bayan ya fado saman gidajen sai suka kama da wuta nan take. Rahotanni sun ce jirgin samfurin King Air 350 yayi wata juyawa ne a lokacin da yake daf da inda zai sauka kwatsam sai ya fado kafin yayi saukar tasa.
Rawalpind, wadda ke kusa da babban birnin kasar Islamabad, can ne inda rundunar sojin Pakistan take da hedikwatarta, kuma jirgin mallakin sojin saman Pakistan ne.
Firai Ministan Pakistan, Imran Khan ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan wadanda suka rasu tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata, kamar yadda gwamnatin kasar ta wallafa a shafinta na tuwita.
Wani ganau wanda al’amarin ya auku a kan idonsa ya ce, “ Jirgin ya yi hatsari ne da misalin karfe 7:00 n asafe agogon GMT, inda ya fada saman wani gida a unguwar Ghulam Khan.
“ Idona biyu lokacin da na ji wucewar jirgin ta saman gidana kuma yana ci da wuta, kafin nan kuma ya fada bisa gidan wasu mutane.” A cewar wani ganau mazaunin unguawar da hatsarin ya faru.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng