Rikicin Shi’a: Iran na tare da magoya bayan El-Zakzaky

Rikicin Shi’a: Iran na tare da magoya bayan El-Zakzaky

-Kasar Iran na goyon bayan mabiya El-Zakzaky dake Najeriya

-A kwanan baya kasar Iran ta rattaba hannu kan wata wasika mai neman a saki Sheikh Ibrahim El-Zakzaky zuwa ga gwamnatin Najeriya

-Iran ta fito fili karara domin ta nuna cewa ta na tare da duk wani dan gwagwarmayar addini dake fadin duniyar nan

Ana cigaba da kai ruwa rana tsakanin mabiya mazahabar Shi’a da gwamnatin Najeriya, yayin da a kullum batun sako malamin ke sanya magoya bayansa yin zanga-zanga.

Ko a makon da ya gabata said a suka gudanar da wata muzaharar matsayin lamba ga gwamnati domin ta sako jagoransu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky wanda aka tsare tun shekarar 2015.

KU KARANTA:El-Zakzaky: ‘Yan Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a birnin Landan

An yi bata kashi tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar ‘yan kungiyar shi’a, lamarin da ya janyo mutuwar babban jami’in ‘yan sanda da wani matashin dan jarida, yayin da mabiya mazahabar shi’a suka yi ikirarin an kashe musu mutane 20.

Rahotanni da dama sun bayyana mana cewa, kasar Iran wadda ke bin tafarkin mazahabar Shi’a na sanya ido kana bin da ke faruwa a Najeriya gameda wannan batu, sannan abu ne wanda Iraniyawa suka dauka da muhimmanci.

Su na kallon irin gwagwarmayar da kungiyar Islamic Movement of Nigeria keyi a matsayin wadanda ke bin tafarkin addini iri guda da mazahabar Shi’a, musamman a daidai wannan lokacin da rashin jituwa ke kara ta’azzara tsakanin mabiya Shi’a da Sunni a kasashen duniya.

Haka zalika, su na amfani da kafafen yada labaran Iran, domin nuna goyon baya ga kungiyar ‘yan uwa musulmi. Sai kuma wani batu na daban da ake ganin ya na taka rawa wajen bai wa kungiyar kwarin gwiwa, wato yadda ‘yan siyasar Iran suka shiga ciki.

Har ila yau, sun taba rubuta wasika wadda yawancin ‘yan majalisar dokokin Iran suka rattabawa hannu aka aikewa gwamnatin Najeriya tare da bukatar ta saki Sheikh Zakzaky domin ya cigaba da rayuwa ta ‘yanci.

Wannan al’amari na IMN bai rasa nasaba da addini da kuma siyasa. Bugu da kari kasar Iran ta bayyana a fili cewa tana goyon bayan duk wani dan gwagwarmayar addini irin El-Zakzaky duk inda yake a fadin duniya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel