Tirkashi: Rashin sunan Ali Nuhu a cikin jerin Ministocin da Buhari ya fitar ya jawo kace - nace

Tirkashi: Rashin sunan Ali Nuhu a cikin jerin Ministocin da Buhari ya fitar ya jawo kace - nace

- Kwanakin baya dai anyi ta yada rade-radin cewa akwai yiwuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bai wa Jarumi Ali Nuhu kujerar Minista

- An bayyana cewa shugaban kasar zai bai wa fitaccen jarumin kujerar ministan matasa da wasanni

- To sai dai kuma wani abin mamaki shine yadda sunayen ya fito babu sunan Ali Nuhu a ciki, hakan ne kuma ya kawo kace-nace a shafukan sada zumunta

A kwanakin baya an yi ta yada jita-jitar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai mika sunan fitaccen dan wasan Hausa na Kannywood Ali Nuhu Mohammed a matsayin Ministan matasa da wasanni.

Sai dai kuma a sunayen shugaban kasar ya bayar domin a tantancewa su babu sunan Ali Nuhu a ciki. Wannan lamari ya janyo kace-nace a kafafen sada zumunta.

Sardaunan Matasan Rijiyar Lemo dake jihar Kano cewa yayi:

"Wai shi Ali Nuhu da ake cewa za a bashi kujerar Minista a karkashin wace jiha zai tashi? Kano, Gombe ko kuma Plataeu?"

KU KARANTA: Allah mai iko: An wayi gari wani babban tafkin ruwa dake kasar Rasha ya rikide ya koma tafkin jini

Haka shi kuma wani shafin Hausa na Facebook mai suna Hausa7 sun sanya hoton Ali Nuhu ne yana fada da wani (kuma akwai yiwuwar an dauki wurin a cikin fim ne) amma sai suka ce daga majiya mai tushe sun jiyo cewa ya fara fada da abokanan aikinsa wanda yake tunanin sune suka yi masa kafar ungulu.

Haka ita ma wata mai amfani da shafin sada zumunta na Facebook mai suna Husnah Ahmad ta sanya hotunan gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da shugaban jam'iyyar jihar Kano na APC, Abdullahi Abbas da kuma Ali Nuhu, inda a karshe tayi wani rubutu na hirar barkwanci kamar haka:

Ali Nuhu: Gwamna ban ji sunana ba cikin ministocin nan?

Ganduje: To kai banda abinka nima ba a saka sunan wadanda na bayar ba.

Ali Nuhu: Au dama baka sanya sunana ba kenan?

Ganduje: Na manta ne.

Audu Ciranci: To kai Ali Nuhu ai nima ba a saka sunana ba!

Ali Nuhu: To ai kai bakada ilimi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel