Sunayen Ministoci: Kin zabar dan asalin Birnin Tarayya akwai takaici - Yan asalin Abuja sun koka

Sunayen Ministoci: Kin zabar dan asalin Birnin Tarayya akwai takaici - Yan asalin Abuja sun koka

-Yan asalin Abuja naganin an maidasu saniyar ware wajen raba mukamai

-Sai dai wata kuma kungiyar matasa, tayi gargadi cewa cikin sunayen wanda za aba mukamin akwai wanda ake tuhuma da cin hanci da rashawa don haka kada a tantance su

Mazauna yan asalin Birnin Tarayya, Abuja bayyana takaici akan rashin sanya daya daga cikinsu a jerin sunaye da shugaba buhari ya aikawa Majalisar Tarayya don tantancewa.

A wani bayani da Danladi Jeji ya rattabawa hannu a madadin sauran kungiyoyin yan asalin Abuja a jiya talata 23, sun bayyana cire su da aka a matsayin nuna wariya daga zamantakewarsu cikin tarayyar Najeriya.

kungiyoyin sun nemi da Majalisar Tarayya ta cire ikon datake da shi akan Majalisar Birnin Tarayya, sannan kuma a cire ikon da shugaban Kasa yake dashi a matsayin gwamnan Abuja.

“ Bamu ji dadi da babu sunan ko daya cikin mazauna yan asalin Birnin Tarayya a jerin sunayen da Shugaba Buhari ya kai Majalisa". Komu bay an kasa bane? Me yasa ake cire wakilcin a majalisar zartarwa? Meyasa wasu jihohi keda sama da mutum daya ko biyu? Inji Jeji acikin bayanin.

KARANTA WANNAN: Zainab da da Mahmud: Bayani game da sabbin ministoci daga jahar Kaduna

Kungiyoyin sunce suna tareda Sanata Philip Aduda da Mambobin Majalisar Wakilai Hon. Micah jiba da Hon. Hassan Usman Sokodabo.

“ Baza mu yarda da wannan wariya ake nunawa yan asalin Birnin Tarayya wanda mune ke karbar bakuncin Jamhuriyar Najeriya”.

Sai dai wata kuma kungiyar matasa, tayi gargadi cewa cikin sunayen wanda za aba mukamin akwai wanda ake tuhuma da cin hanci da rashawa don haka kada a tantance su.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook:https://facebook.com/legitnghausa

Twitter:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel