Da zafi-zafinsa: Anyi awon gaba da wasu mutum 3 kan babbar hanyar Legas-Ibadan

Da zafi-zafinsa: Anyi awon gaba da wasu mutum 3 kan babbar hanyar Legas-Ibadan

-Yan bindga sun sace mutum uku kan hanyar Legas zuwa Ibadan ciki hadda dan gidan Dr Sule mai asibitin Lafia Hospital dake Apata a garin Ibadan

-Yan bindigan su 15 ne mutum daya ne kacal cikinsu ya iya magana da turanci sauran kuwa sai dai hausa kamar yadda daya daga cikin wadanda suka kubuta ya bamu labari

A daren jiya Talata ne aka yi awon gaba da wasu mutum uku wadanda ke tafiya kan babbar hanyar Legas-Ibadan inda suke tafe cikin mota kirar Toyata Sienna.

KU KARANTA:Anyi arangama tsakanin 'yan bindiga da sojin NAF a Kaduna har jami'ai 2 sun mutu

Daya daga cikin fasinjojin da ya samu kubuta ya ba wakilin jaridar Punch labarin cewa, ‘yan bindigan su 15 ne, kuma hausa kawai suka iya banda mutum guda cikinsu wanda shi kadai ya iya yaren turanci.

Daya daga cikin wadanda aka sacen da ne wurin Dakta Sule mamallakin Lafia Hospital Apata, yayinda sauran biyun kuma ma’aikatan asibitin ne.

Wakilin jaridar Tribune Online wanda ya samu zantawa da wani ma’aikacin asibitin, ya bamu labarin cewa tabbas an sace wadannan mutum uku.

Haka zalika wata majiyar ta bamu labarin cewa, da safiyar yau Laraba ne wani rubutacce sako keta yawo a shafunka sada zumunta na WhatsApp, ga kuma abinda sako ya kunsa: “ Ina kwana da fatan kun tashi lafiya, a yanzu haka akwai ‘yan bindiga kan hanyar Legas-Ibadan. Da safiyar yau din nan nake samun sako daga wurin abokina, Dr Sule mai asibitin Lafia Hospital Apata, Ibadan, inda ya rubuto cewa, ku taimakin da addu’a an sace babban dana da ma’aikatana biyu yayinda suke hanyar dawo Ibadan daga Legas.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel