Deen Muhammad Sheikh, malamin da ya musuluntar da mutane 1,08,000

Deen Muhammad Sheikh, malamin da ya musuluntar da mutane 1,08,000

-Deen Muhammad Sheikh, wani bawan Allah dan addinin Hindu da ya musulunta a kasar Pakistani sa'annan ya musuluntar da mutane 1,08,000

-An haifi Muhammad Sheikh a shekarar 1942 a cikin ahalin Hindu a garin Badin Sindh na kasar Pakistan. Muhammad Sheikh ya musulunta a shekarar 1989 tare da wani kawunshi

-Deen Muhammad ya ce babban burinshi shine ya ga duk duniya an zama musulmai

Babu shakka addinin musulunci shine addi mafi saurin habbaka a fadin duniya. Tun bayan saukar da Al-kur’ani mai tsarki, Allah na shiryar da mutane zuwa hanya madaidaiciya, ko ta hanyar yakar garuruwan mutanen da ba musulmai ba ko kuma ta hanyar da’awa.

Musulmai da yawa sun taimaka sosai wajen yada addinin musulunci. Tun shekaru 1,400 da suka wuce musulmai sun dauki da’awa a matsayin babbar hanyar bautawa Allah (S.W.T). malamai da yawa sun sha wahala sosai a dalilin yin kira zuwa ga addinin musulunci, amma hakan bai sanya sun daina yin kira zuwa ga addinin musulunci ba.

Daya daga cikin wadannan malaman sun hada da Deen Muhammad Sheikh, wanda shi ma musulunta yayi. Shi ka dai ranshi ya musuluntar da mutane 1,08,000.

An haifi Muhammad Sheikh a shekarar 1942 a cikin ahalin Hindu a garin Badin Sindh na kasar Pakistan. Muhammad Sheikh ya musulunta a shekarar 1989 tare da wani kawunshi. Tun bayan hakan ne ya fara kiran mutane zuwa ga addinin musulunci inda kuma yayi nasarar musuluntar da mutane sama da dubu dari.

Shine shugaban masallacin Jamia da islamiyyar Aisha Ta’aleemul Qur’an, makarantar da ake musuluntar da mutane.

Sheikh Muhammad ya fara rayuwar musulunci da kuruciyarshi, a lokacin da yake boyewa yana karanta Qur’ani saboda yana tsoran mutane su ganshi.

Ya bayyana cewa : “Na dade ina son musulunci. Na karanta Al-qur’ani mai girma na kuma gane cewa abubuwan bauta 360 ba su da wani anfani a gare ni”

Iyalanshi sun ji tsoran kada ya musulunta musamman mahaifiyarshi da ta aurar da shi ta yadda cewa zai daina tunanin musulunci ya mayar da hankalinshi kan rayuwar aure.

Sheikh Muhammad ya auri wata yarinya yar Hindu amma soyayyarshi ga musulunci ba ta gushe ba. Bayan tsawon lokaci sai ya yanke hukuncin ya musulunta. Iyalanshi sun saka mashi karan tsana illa kawunshi guda daya da suka karbi musulunci tare a shekarar 1989.

Muhammad ya samu wani malami, Muhammad Jangi wanda ya koyar da shi Al-Qur’ani da kuma hadisin annabi (SAW). Ya fara da’awa a cikin gidanshi, sa’annan ya shiga cikin ahalinshi da ga nan kuma ya shiga cikin al’umma. Baiwar da Allah ya mashi ta iya da’awa ya sanya ya musuluntar da mutane 1,08,000.

KARANTA WANNAN: Babban Bankin Najeriya ya yi hadaka da masallatai da cocina don koyar da ilimin sarrafa kudade

Attajiran musulmai da yawa sun taimaka mashi da kudade sosai wajen gudanar da da’awarshi. Haka zalika sun sha yi mashi tayin kudade, amma sai ya kiya ya ce su samar wa sababbin musulmai aiki da kudin.

Ya bayyana cewa: “Babban burina shine inga duk duniya an zama musulmai.”

Tun lokacin da ya fara kira zuwa musulunci, ya yi suna sosai kuma hakan ya sanya mutane da yawa na ziyartarshi har gida don su musulunta. Ya taimakawa sababbin musulmai duk ta hanyar da ya kamata. Ya na sama masu wajajen zama, sa’annan ya koya masu abubuwan farko na addini kamar su tsarki da salloli.

Sheikh Muhammad ya ajiye takardar sunaye da bayanai kamar su adireshi da nambar waya na duka mutane 1,08,000 da suka musulunta a wajenshi.

Sheikh Muhammad bashi da niyyar daina kiran mutane zuwa musulunci kuma bai damu da yawan mutanen ba. Ya dauki maganar da ya fada na cewa yana so ya ga duk duniya ta musulunta da gaske har cikin zuciyarshi.

Allah ubangiji ya taimake shi ya biya mashi bukatunshi.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel