Fasto Felix ya goyi bayan MURIC, ya yi kira da a dakatar da shirin BB Naija

Fasto Felix ya goyi bayan MURIC, ya yi kira da a dakatar da shirin BB Naija

-Fasto Felix Ajide na cocin King Jesus ya bayyana cewa shirin wasan BB Naija da ake haska abun da ke faruwa da gaske na taimakawa wajen lalata tarbiyya

-Ya kara da cewa shirin ba shi da wani amfani ga tarbiyya, sa’annan yayi kira da a dakatar da shirin

-Felix ya kuma ce kamata yayi a yi amfani da kudin da ake kashewa wajen gudanar da shirin don a kawo ababen ci gaba ga al’umma

Fasto Felix Ajide na cocin King Jesus ya bayyana cewa shirin wasan BB Naija da ake haska abun da ke faruwa da gaske na taimakawa wajen lalata tarbiyya, kuma bai dace da al’ummar mu ba.

Ajide ya bayyana ma kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) hakan a Abuja, jiya Juma'a 19 ga watan Yuli 2019, ya ce shirin na nuna batsa karara, ya kara da cewa shirin ba shi da wani amfani ga tarbiyya, sa’annan yayi kira da a dakatar da shirin.

Ya ce kamata yayi a yi amfani da kudin da ake kashewa wajen gudanar da shirin don a kawo ababen ci gaba ga al’umma.

Ya ce : “Kama ta yayi a dakatar da shirin, saboda babu wani abun kwaikwayo a cikinshi, rashin tarbiyya ce kawai muke kallo a ciki.”

Ya kara da cewa : “Idan kasashen turai na yinshi, ba dole bane muma sai anyi shi a Najeriya, muna bukatar ceto a kasar nan.”

KARANTA WANNAN: Wahalar rayuwa ta sanya mahaifiyar tsohon dan wasan Najeriya Rashidi Yekini fara sayar da biredi a titi

Wata mata da ta bukaci a boye sunanta, ta ce ba dole bane sai an dakatar da shirin. Ta ce “Don me zai sa a ce a dakatar da shi. Ba dole bane sai ka kalla, ko kuma ka fita daga tsarin tashar idan har ya saba maka.”

“Mafi yawancin abinda mutane ke korafi a kanshi, kamar bangaren bayan gida an daina haska su.”

Ta kara da cewa “Ya samar da hanyar da za a nuna al’adunmu, sa’annan ya samar wa da mutanenmu hanyar da za su tallata kayansu su kuma kara ma kayansu daraja.”

Kungiyar kare yancin musulmai (MURIC) ta bayyana cewa shirin babu tarbiyya a cikinshi, shaidanci ne sa’annan ta ce ba ta san dalilin da ya sanya ministirin labarai da al’adu ba ta yi komai akan shirin ba.

Haka zalika da ta ke magana, wata ma’aikaciyar gwamnati mai suna Chinonye Anokam ta ce shirin na baiwa matasa dama su gano basirar da Allah ya yi masu sa’annan su kuma cimma burinsu.

Ta ce: “Ba lallai ba ne ka san basirar da Allah ya yi maka ba, amma shirin na samar da dama ga mutane su san basirar da Allah ya yi masu.”

Shima da yake tofa albarkacin bakinshi, Mustapha Suleiman, dan kasuwa ya ce babu tarbiyya a shirin sa’annan ya ce ya na goyan bayan da a dakatar da shirin. Ya kara jaddada cewa babu wani abun mai kyau da mutum zai koya daga shirin. Ya kara da cewa wasu yan wasan shirin na nuna rayuwar karya.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel