Aiki gadan gadan: Gwamna Babagana Zulum zai gina gidaje 400

Aiki gadan gadan: Gwamna Babagana Zulum zai gina gidaje 400

-Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya kaddamar da aikin gina gidajen zama 400 a karamar hukumar Mafa dake a jihar Borno

-Haka zalika gwamnan ya kaddamar da rabon kayan aikin gona ga mutanen da ke zaune a sansanin yan gudun hijira a garin

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya kaddamar da aikin gina gidajen zama 400 a karamar hukumar Mafa dake a jihar Borno.

Gwamnan ya dawo mahaifarshi, karamar hukumar Mafa, jim kadan bayan da ya gama zagaye duka kananan hukumomin jihar Borno, inda ya kaddamar da aikin gina gidajen zama 400 a Ajiri.

Haka zalika gwamnan ya kaddamar da rabon kayan aikin gona ga mutanen da ke zaune a sansanin yan gudun hijira a garin.

Bugu da kari, gwamna Zulum ya duba aikin gyara wajen shakatawa na Dikwa wanda ya bayar da umurnin a mayar da shi wajen koyan sana’o’i.

Gwamnan wanda ke zagayen gani da ido a wasu kananan hukumomi, ya duba ayyukan gona da akeyi a wajajen, musamman rabon kayan aikin noma ga manoma.

KARANTA WANNAN: Jerin hanyoyi 24 da shugaba Buhari ke yi a fadin kasar nan

Haka zalika, ya duba aikin gyaran titunan kananan hukumomin Mafa, Dikwa da Ngala. Ya bayyana cewa ayyukan na da mahimmanci saboda zai habbaka hada hadar kasuwanci a yankunan, da ma makwabtan kasashe kamar Kamaru, Nijar da Chadi.

Ya bayyana cewa : “Na yi matukar murna, na ji dadi sosai da na ga yadda aikin ke tafiya daga Gajibo na Karamar hukumar Dikwa”

Gwamnan ya yabawa hukumar gyara tituna ta jihar da kuma ministirin ayyuka ta jihar. Ya ce : “Za mu tabbatar da cewa an cigaba da irin wannan aikin ta yadda da zarara kakar ruwan sama ta wuce, sai a shinfida kwalta mai laushi ba tare da wata matsala ba.”

Gwamnan ya yi alkawarin kammala duk wani aikin gyaran titi cikin shekaru biyu zuwa uku. Jaridar Kanem Trust ta gano cewa gwamnan na neman gwamnatin tarayya ta bashi izini ya gyara titunan Maiduguri zuwa Bama zuwa Banki da titin Maiduguri zuwa Gamboru zuwa Ngala wadanda titunan gwamnatin tarayya ne.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel