An gurfanar da wani direban Keke Napep a gaban kotu saboda ya saci Keke Napep guda biyar

An gurfanar da wani direban Keke Napep a gaban kotu saboda ya saci Keke Napep guda biyar

-A yau Alhamis 18 ga watan Yuli 2019, an gurfanar da wani direban adai daita sahu mai suna Azeez Adepoju a gaban kotun majistire dake a Yaba jihar Legas a bisa zarginsa da satar Keke Napep guda biyar

-Oriabure ya yi ikirarin cewa wanda ake karar ya sace adai dai ta sahu guda biyar da wani Abdurrahman Kabiru ya bashi a kan tsarin facez

-Mai shari’ar, S. O Obasa ta bayar da wanda ake karar beli akan kudi Naira 500,000 da kuma mutane biyu da za su tsaya mashi

A yau Alhamis 18 ga watan Yuli 2019, yan sanda sun gurfanar da wani direban adai daita sahu (Keke Napep) mai suna Azeez Adepoju mai shekaru 32 a gaban kotun majistire dake a Yaba jihar Legas a bisa zarginsa da satar Keke Napep guda biyar da kudinsu ya kai Naira miliyan 5.5.

Dan sanda mai gabatar da kara, sajan Godwin Oriabure ya bayyana ma kotun cewa wanda ake karar ya aikata laifin ne a ranar 6 ga watan Agusta 2018 a unguwar Mushin ta jihar Legas.

Oriabure ya yi ikirarin cewa wanda ake karar ya sace adai dai ta sahu guda biyar da wani Abdurrahman Kabiru ya bashi a kan tsarin facez.

A cewar dan sandan mai gabatar da kara, Abdurrahman ya baiwa Azeez Keke Napep biyar, kowanne akan kudi Naira miliyan 1.1, don ya bayar da su akan tsarin facez.

Ya bayyana cewa sun yi yarjejeniya akan cewa Azeez ya samo direbobin da za su rinka tuka Keke Napep din, sa’annan duk sati ya kaiwa Abdurrahman Naira 20,000 daga kowanne Keke Napep guda.

KARANTA WANNAN: Yan iska sun far ma ayarin wani basaraken Yarbawa kan rigimar fili

Oriabure ya bayyana cewa wanda ake karar ya gaza kaiwa Abdurrahman ko Kobo sa’annan ya daina daukar kiran waya daga wajen Abdurrahman.

Oriabure ya bayyana cewa laifin ya saba ma sashe na 287 (7) na dokar laifuffuka da hukuncinsu na jihar Legas. Hukuncin laifin kamar yadda sashen ya zayyana zai kasance shekara bakwai a gidan yari.

Mai shari’ar, S. O Obasa ta bayar da wanda ake karar beli akan kudi Naira 500,000 da kuma mutane biyu da za su tsaya mashi. Ta dage sauraran karar zuwa ranar 30 ga watan Yuli 2019. (NAN)

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel