Kungiyar kwadago za ta shiga yajin aiki idan har gwamnati bata dawo teburin sulhu ba

Kungiyar kwadago za ta shiga yajin aiki idan har gwamnati bata dawo teburin sulhu ba

-Kungiyar kwadago ta yi kira ga mambobinta a duka jihohi 36 da babban birnin tarayya da su shirya shiga yajin aiki

-kungiyar ta bukaci gwamnati da ta gaggauta dawo wa kan teburin sulhu don a kammala tattaunawa don ganin kowanne ma’aikaci ya anfana da saban tsarin mafi karancin albashi

Kungiyar kwadago ta yi kira ga mambobinta a duka jihohi 36 da babban birnin tarayya da su shirya shiga yajin aiki idan har gwamnati ta karya yarjejeniyar da aka kulla kan saban mafi karancin albashi.

Haka zalika, bayan da kungiyar ta gama tattaunawa da zauren sulhunta ma’aikatan gwamnati na kasa, ta rage bukatunta na a kara 66.66% zuwa kashi 30% dangane da ma’aikata dake a mataki na 07 zuwa na 14 sa’annan ta mayar da shi kashi 25% ga ma’aikatan dake a mataki na 15 zuwa na 17.

Ta fannin gwamnati kuma, ta nace cewa lallai lallai karin kashi 9.5% kawai za ta yi ga ma’aikatan dake a mataki na 07 zuwa na 14, dangane da ma’aikatan dake a mataki na 15 zuwa 17 kuma karin kashi 5% kawai za tayi.

Ma’aikatan sun bayyana damuwarsu cewa a maimakon bangaren gwamnati ya kawo matsayar da aka cimmawa: “Abin mamaki bayan da kwamitin suka dawo sai bangaren gwamnati suka shigo da wani bakon sashe a cikin zantawar inda suka nace cewa an ba kwamitin umurnin da yayi gyaran albashin ma’aikatan ta yadda zai yi dai-dai da kasfin kudin 2019.”

Kungiyar yan kwadago tayi duk iya kokarinta na ganin ta maido bangaren gwamnati akan asalin yarjejeniyar da ake tattaunawa a kai amma abin ya ci tura.”

KARANTA WANNAN: Yadda mara lafiya ya kashe kansa da gilashin taga a asibitin UBTH

A takardar da kungiyar ta fitar, wacce aka baiwa manaima labarai, kungiyar ta bayyana cewa ta rage bukatunta ne bayan da gwamnati tayi alkawarin cewa za ta gyara albashin ma’aikata baki daya ba da jimawa ba.

Mukaddashin shugaban kungiyar, Kwamared Anchaver Simon da sakataren kungiyar Alade Bashir Lawal ne suka sanya ma takardar hannu.

A takardar, kungiyar ta bukaci gwamnati da ta gaggauta dawo wa kan teburin sulhu don a kammala tattaunawa don ganin kowanne ma’aikaci ya anfana da saban tsarin mafi karancin albashi da shugaban kasa ya amince da shi a matsayin doka tun cikin watan Afirilun 2019.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel