Jarumar fina finan hausa, Nafisa Abdullahi za ta zama daraktar fina finai

Jarumar fina finan hausa, Nafisa Abdullahi za ta zama daraktar fina finai

- Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa za ta bada umurni a wani wasan kwaikwayo karo na farko a matsayin darakta

-Jarumar za ta bada umurnin shirin a karkashin kamfaninta mai suna ‘Nafs Production’

-Nafisa Abdullahi ta samu sakonnin taya murna a shafin ta na dandalin sada zumunta fiye da 300 daga wajen abokan aiki da masoya.

Yar wasan kwaikwayo ta Kannywood, Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa za ta bada umurni a wani wasan kwaikwayo karo na farko a matsayin darakta.

A ranar Juma’a ta bayyana cewa “Ina bukatar addu’ar ku. Zan hau kujerar mai bada umurni karo na farko.”

Nafisa Abdullahi za ta bada umurnin shirin a karkashin kamfaninta mai suna ‘Nafs Production’ inda za ta kula da sabon shirin mai suna ‘Zainab Ali’.

Nafisa Abdullahi sananniyar yar wasan kwaikwayo ce musamman saboda kwarewarta wajen takara rawa daban daban a fina finai.

Fim din farko da ya fara fito da Nafisa Abdullahi shine wannan fim din mai shauki da mutane suka yaba mawa mai suna ‘Dan Marayan Zaki’.

A fim din Dan Marayan Zaki, Nafisa Abdullahi ta fito a matsayin yar sarki da ake so a tilasta mata auren dan wani attajiri da bata so.

Nafisa Abdullahi, baya ga wasan kwaikwayo na Hausa, ta na kuma yin tallace tallace ga kamfanoni daban daban.

KARANTA WANNAN: Yanzu-yanzu: Atiku ya yi tir da kisar gillar da aka yi wa diyar Farosanti

Bayan da ta yi sanarwa a shafin ta na instagram, abokan aikinta da masoyanta da dama sun ta yi mata addu’o’i da fatan alkhairi a sabon aikin da za ta a fara na matsayin mai bada umurni a fina finai.

Daraktan fina finan Hausa, Naziru Danhajiya, shine mutum na farko da yayi saurin tofa albarkacin bakinsa a shafin. Ya taya ta murna ya kuma yi mata fatan alkhairi.

Yar wasan hausa, Zainab Booth, ita ma tayi rubutu a shafin da hausa inda ta ke yi ma Nafisa Abdullahi fatan alkhairi.

Nafisa Abdullahi ta samu sakonnin taya murna a shafin na ta fiye da 300 daga wajen abokan aiki da masoya.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel