MURIC tayi Allah wadai da shirin BB Naija

MURIC tayi Allah wadai da shirin BB Naija

-Kungiyar MURIC ta bayyana cewa shirin BB Naija na tallata rashin tarbiyya da batsa a kasar nan.

-Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi maza maza ta haramta shirin

-MURIC ta kuma yi kira da kungiyar kiristoci da ta zo a hada karfi da karfe wajen dakatar da shirin

Kungiyar kare hakkin musulmai (MURIC) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi maza maza ta haramta shirin ‘Big Brother Naija’.

MURIC ta bayyana cewa shirin wanda ake haska abinda ke faruwa da gaske na tallata rashin tarbiyya da batsa a kasar nan.

Daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ya bayyana cewa dole a kama shirin da laifin tallata rashin kungiya da dabbaka tabarbarewar al’ada.

KARANTA WANNAN: Ban ce Buhari zai gabatar da sunayen ministoci a wannan makon ba – Lawan

Ya bayyana cewa “Ana tura mu cikin duniyar tsiraici da rashin kungiya da tsiya. Mutanen cikin gidan BB Naija na sun batar juna a bude suna saduwa da juna a fili. Shirin BB Naija iskanci ne, rashin kunya ne. Annoba ce ga kowanne gida. Shaidanci ne da ba za mu yadda da shi ba.”

Ya kara da cewa “Ina al’adunmu da dabi’un mu? Wannan na daga cikin al’adun nahiyar Afirika a rinka yin jima’i a fili? Ina hukumomi suke? Hukumar sadarwa da al’adu na bacci ne? Wa zai kare yaranmu daga wannan mummunan harin? Waye ya yima kasar mu haka?”

MURIC tayi kira ga kiristocin kasar nan da su zo a hada hannu wajen yin Allah wadai da wannan shirin a kuma tilastawa gwamnati ta dakatar da shirin.

Ya bayyana cewa “Za mu iya kawo karshen wannan iskancin da ake kira da BB Naija idan musulmai da kiristoci za su hada karfi da karfe wajen ganin an yaki wannan shaidancin. Gida dai gida ne. Babu addinin da ya yadda da rashin kunya.”

MURIC ta bukaci ministirin al’adu da tayi maza maza ta dakatar da wannan rashin kunyar da ake yi a Najeriya.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel