Allah wadan naka ya lalace: Wani mutumi ya shekara biyu yana zina da 'yar cikinsa, yayin da yake sanyata ta zubar da ciki idan ya shiga

Allah wadan naka ya lalace: Wani mutumi ya shekara biyu yana zina da 'yar cikinsa, yayin da yake sanyata ta zubar da ciki idan ya shiga

- An wallafa labarin wani mutumi a shafin Twitter, wanda yake kwanciya da 'yarshi ta cikinsa na tsawon shekaru biyu

- Bayan haka kuma mutumin yana tilasta 'yar tashi domin ta zubar da ciki a duk lokacin da ciki ya shiga

- An wallafa labarin ne domin neman mafita akan lamarin, inda mutumin ya bukaci jin ta bakin jama'a

Wani mutumi ya wallafa wani labari a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana cewa ya gano yadda dan uwanshi yake kwanciya da 'yarshi ta cikinsa, kuma mahaifiyar yarinyar tayi shiru ta kasa magana.

Mutumin ya ce 'yar gidan mutumin mai suna Chimezie, wacce take da shekaru 17 a duniya, ta bayyana cewa mahaifinta ya shafe shekaru biyu yana yi mata fyade, sannan sau uku yana tilasta ta akan ta zubar da cikin da yake yi mata.

KU KARANTA: Tirkashi: 'Yan bindiga sunyi garkuwa da wasu turawa guda biyu, sun kuma kashe dan sandan da yake gadinsu

Amma wani abin mamaki shine, mahaifiyar yarinyar taki yadda da maganar yarinya, tana goyon bayan duk wani abu da mahaifin yarinyar ya fada.

Mutumin da ya wallafa labarina shafin Twitter yana bukatar jin ta bakin mutane akan lamarin.

Mutane da yawa sunyi Allah wadai da lamarin, inda wasu suke ganin laifin mahaifiyar kan yadda ta yi shiru da bakinta yayin da ake cin zarafin 'yarta.

Wasu kuma sun bukaci yarinya ta kai kara kotu domin abi mata hakkinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel