Madallah: Matar gwamnan Bauchi ta gina azuzuwa, gada da Masallaci a wasu kauyuka

Madallah: Matar gwamnan Bauchi ta gina azuzuwa, gada da Masallaci a wasu kauyuka

-Matar gwamnan jihar Bauchi Hajiya Aisha Bala Muhammad ta gina wasu azuzuwan karatu da masallaci da gada a wasu kauyuka a Bauchi

-An gudanar da wannan aiki ta hanyar gidauniyar matar gwamnan mai suna Al-Muhibbah

-Matar gwamnan ta yi kira ga al'ummar da suka amfana da aikin da su yi amfani da gine ginen ta hanyar da ta dace

Matar gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Aisha Bala Muhammad, ta gina masallaci da azuzuwan karatu guda uku da kuma gada a wasu kauyuka dake a karamar hukumar Bauchi.

An gudanar da wadannan ayyuka a kauyukan Gursumi, Kangere da kuma Inkil da ke a karamar hukumar Bauchi.

An yi wadannan ayyukan ne ta hanyar kungiyar uwar gidan gwamnan mai suna Gidauniyar Al-Muhibbah, wacce aka kirkira shekaru da yawa da suka wuce tun lokacin da mijinta ke ministan babban birnin tarayya.

Da take bayani a lokacin da ta kai ziyara a kauyukan da suka amfana da aikin, Hajiya Aisha ta ce an gudanar da aikin bayan da kauyukan suka bukaci da ayi masu.

KARANTA WANNAN: An gano yarjejeniyar da aka kula tsakanin Goje da Shugaba Buhari kafin ya janye takararsa

Ta kuma yi kira ga kauyukan da su kula da ayyukan kuma su yi amfani da su ta hanyar da ta dace. Ta kuma basu tabbacin cewa gwamnatin mijinta za ta ci gaba da samar wa da mutanenta ababen more rayuwa sa’annan kuma ta bukace su da su ci gaba da bada goyan baya ga gwamnatin jihar karkashin jagorancin mijinta.

Da yake maida jawabi, hakimin Galambi, Alhaji Shehu Adamu Jumba da wakilan sauran kauyukan da suka amfana da aikin, sun godewa matar gwamnan da ta samar masu da gine ginen, inda suka bayyana cewa gine ginen na da matukar mahimmanci ga rayuwarsu.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel