Gwamnan Taraba ya amince da hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane
-Gwamna Darius Ishakyu ya rattafa hannu a dokar magance garkuwa da mutane wadda ta bayar da hukuncin kisa ga masu aikata laifin
-Hakan ya biyo bayan da majalisar jihar Taraba ta yi garanbawul ga dokar hana garkuwa da mutane
-Jihar Taraba na fama da yawan garkuwa da mutane a yan kwanakin nan
Sakamakon yawan garkuwa da mutane da ake yi a jihar Taraba da wasu jihohi a fadin Najeriya, gwamna Darius Ishaku ya rattafa hannu a dokar da majalisar jihar tayi wanda ta bayar da hukuncin kisa da kuma daurin rai da rai ga masu aikata garkuwa da mutane.
Mai taimakawa gwamnan akan harkokin yada labarai, Bala Dan Abu ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ga manaima labarai.
Bayanin ya kara da cewa, kudirin dokar ya fito ne daga wajen kakakin majalisar jihar, Peter Abel Diah, kuma an tabbatar da kudirin ya zama doka bayan da sauran yan majalisun suka amince da shi.
KARANTA WANNAN: Shugaba Buhari zai kaddamar da gangamin hana bayan gida a fili
Jawabin yana cewa kamar haka ”A karkashin sabuwar dokar, duk wanda aka kama da laifin aikata garkuwa da mutane a jihar, to zai fuskanci hukunmci mafi tsanani.”
“Wannan dokar matakin gwamnati ne na magance matsalolin tsaro, musamman laifin garkuwa da mutane don karbar kudin fansa, wanda yanzu ya zama ruwan dare a jihar da wasu sassa a Najeriya.”
Legit.ng ta ruwaito cewa majalisar jihar ta Taraba, ta yi garanbawul ga dokar hana garkuwa da mutane ta shekarar 2010 inda yanzu ta bayar da hukuncin kisa da daurin rai da rai ga duk wanda aka kama yana aikata laifin.
Shugaban masu rinjaye na majalisar kuma dan majalisa mai wakiltar yankin Karim Lamido ne ya gabatar da kudirin, daga bisani kuma Alhaji Bashir Mohammed, shugaban marassa rinjaye ya mara mashi baya.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng