Kisan ‘yan Najeriya a Libya dabbanci ne da keta, inji Buhari
-Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da harin jirgin sama da aka kai a cibiyar 'yan ci rani dake Tripoli
-Buhari ya bayyana bacin ransa akan lamarin inda ya bayyana shi a matsayin dabbanci da keta
-Shugaban Najeriyan ya yi kira ga hukumomin tsaron kasar Libya da su fara gudanar da bincike domin zakulo wadanda suka aikata wannan ta'adi kana a gurfanar da su gaban kotu
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin inda ya ce wannan harin ba komi cikinsa in banda “ dabbanci da keta.”
Rahotanni sun nuna cewa an kashe akalla mutane 40, yayin da wasu 80 suka ji raunuka iri daban-daban a harin bam wanda ya tarwatse a wata cibiya dake gabashin birnin Tripoli.
KU KARANTA:Iran za ta inganta karfin makamashin nukiliyarta, inji Shugaban kasar
‘Yan Najeriya da dama ne suka rasa rayukansu a harin wadanda suke a kasar domin yin ci-rani. Burinsu shi ne tsallakawa nahiyar Turai daga Libyan domin samun rayuwa mayalwaciya.
A wani bayyani da Shugaban ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba, ya ce akwai bukatar a gudanar da bincike na musamman kan harin wanda aka kai shi ta sama.
Ga abinda Shugaban ya fadi: “ Harin sama da aka kai sansanin ‘yan ci-rani a birinin Tripoli dabbanci ne mai cike da keta da kuma rashin tausayi. Tabbas ya zama wajibi a yi bincike kan lamarin domin a gurfanar da masu laifin gaban kotu.”
Bugu da kari, tarzoma da rabuwar kai sun daidaita a Libya tun bayan kashe Shugaba Mu’ammar Gaddafi a shekarar 2011.
Usama Ali, mai magana da yawun hukumomin bayar da agaji ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, harin ya taho ne kai tsaye daga Tajoura inda ya fado cibiyar da ake tsare ‘yan ci-rani 120.
A cewarsa, babu mamaki mamatan sun fi 40 domin kuwa kididdigar farko ce kawai akayi aka samu wannan adadin.
Gwamnatin National Accord mai samun goyon bayan majalisar dinkin duniya wadda Fira minister Fayez ai Serra ke jagoranta ta zargi dakarun Libyan National Amry da kai wannan hari na safiyar Laraba.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng