An tsare wasu mutane 3 bayan sun yi wa dan sanda dukan tsiya har lahira

An tsare wasu mutane 3 bayan sun yi wa dan sanda dukan tsiya har lahira

Wata kotun Majistare da ke Iyaganku a Ibadan a ranar Talata, 2 ga watan Yuli ta bayar da umurnin kulle wasu mutane uku wadanda ake zargi da laifin dukan wani dan sanda har lahira har zuwa lokacin da za a ji shawarar doka.

Alkalin kotun, Misis Mercy Amole-Ajimoti, ta bada umurnin cewa a rufe Abubakar Mohammed mai shekaru 25; Salisu Usman mai shekaru 20 da Ajayi Oji dan shekaru 32 a kurkukun Agodi.

Amole-Ajimoti wacce ta ki sauraron rokon wadanda ake tuhuma, ta bukaci yan sanda dasu mayar da fayil din karar zuwa ga hukumar DPP na jihar Oyo.

Har ila yau ta dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Yuli.

Inspekta Sunday Ojeleye, ya fada ma kotu cewa masu laifin guda uku sun hada kai wajen aikata kisan a ranar 22 ga watan Maris, da misalin karfe 7:00 na yamma a yankin Sabo, Momola, Ibadan.

Ojeleye yayi zargin cewa masu laifin sun ci zarafin Inspekta Tirimisiyu Akinola, da mugayen makamai a Sabo, yayin da yake bakin aiki cikin duhu.

Mamacin ya kasance dan sandan yankin Iyaganku, Ibadan, ya kuma jagorancin yan sanda zuwa Sabo.

KU KARANTA KUMA: Aiki ga mai kare ka: Rundunar sojin sama ta kashe 'yan bindiga guda 20 a dajin Zamfara

Dan sanda mai karan yace laifin ya saba ma sashi na 316 na doka kuma hukuncinsa yazo a karkashin sashin 319 da 324.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng