Gawar wani da ya boye a tayar jirgi ta fado daga sararin samaniya
-Gawar wani mutum ta fado daga cikin jirgin sama na Kenyan Airways a lokacin da yake kan hanyar zuwa Landan
-Yan sandan Landan sun bayyana cewa ana zaton ya boye ne a cikin tayar jirgin bayan da suka gano wata jika da kayan sawa a tayar hagu ta jirgin saman
-Hukumar jirgin saman na Kenyan Airways sun bayyana cewa babau wata matsala da ta samu jirgin
A yau Talata 2 ga watan Yuli 2019, gawar wani mutum da ya boye a tayar jirgin Kenyan Airways ta fado daga sararin samaniya a lokacin da jirgin ke kan hanyar zuwa Landan.
Gawar mutumen ta fado a lambun wani gida dake a Clapham, kudancin Landan, kilo mita 27 kafin a kai filin jirgi na Heathrow a garin Landan, wanda hakan ya tsorata masu gidan, inda su kayi maza suka kira yan sanda.
Daga baya yan sandan sun gano wata jika dauke da abinci da kayan sawa a tayar hagu ta jirgin saman Kenyan Airways da ya sauka a filin jirgin sama na Heathrow.
KARANTA WANNAN: Ginin majalisa na barazanar rushe wa - Gbajabiamila
Mai magana da yawun hukumar yan sandan Scotland Yard, ya ce ana zaton cewa mutumen ya boye ne cikin tayar jirgin kuma ya fado ne a lokacin da jirgin ya fitar da taya zai sauka a filin jirgi na Heathrow.
Ya kara da cewa babu wani bayani game da mutumen.
Jami’an Kenyan Airways sun bayyana cewa an duba jirgin amma babu wata matsala da ta samu jirgin.
Indai za a iya tunawa, a ranar Asabar 24 ga watan Agusta 2013 wani yaro dan shekara 13 mai suna Daniel Ohikhena daga Owan a jihar Edo ya boye a cikin jirgin Arik da ya taso daga jirgin sama na Benin zuwa Legas.
Bayan da jirgin ya sauka a Legas ne jami'an tsaro da fasinjoji suka sha mamaki ganin yaron na saukowa. Daniel ya bayyana ma yan jarida cewa ya dauka jirgin Amerika za shi saboda yana so ya bar Najeriya.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng