DSS, 'yan sanda, da sojoji sun yi dirar ninja a ginin COZA, Abuja

DSS, 'yan sanda, da sojoji sun yi dirar ninja a ginin COZA, Abuja

Jami'an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) cikin shiga irin ta ninja, dakarun soji, jami'an 'yan sanda da na hukumar 'civil defence' sun yi dirar mikiya a ginin wata Coci 'Commonwealth of Zion Assembly (COZA)' da ke Abuja.

Wakilin jaridar Punch da ke wurin ya ce a kalla jami'an tsaro 50 a cikin motocin sintiri sun yi cirko-cirko da makamansu a hannu a gefen hanyoyin titin Nasir El-Rufa'i da ginin Coci ya ke.

Punch ta kara da cewa duk da a kan ga jami'an tsaro a harabar Cocin kowacce ranar Lahadi, adadin jami'an tsaron da aka gani yau ya wuce na ko yaushe.

Ana ganin cewa tura jami'an tsaron ba zai rasa nasaba da barazanar da wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama suka yi ba na gudanar da zanga-zanga a harabar Cocin biyo bayan zargin babban limamin Cocin COZA, Abiodun Fatoyinbo, da aikata fyade.

DUBA WANNAN: Ina daukan nauyin mata na 3 da yara 11 daga garkuwa da mutane - Sani Ibrahim

A ranar juma'a ne uwargida Busola Dakolo, matar fitaccen mawaki, Timi Dakolo, ta zargi Fatoyinho da yi mata fyade shekaru 20 da suka gabata.

Batun zargin fyaden ya jawo barkewar cece-kuce tare da kiraye-kirayen kungiyoyi a kan a kama Fatoyinho, a gefe guda kuma masu goyon bayansa sun lashi takobin kare shi.

Kazalika, limamin Cocin COZA, ya musanta dukkan zargin da ake yi masa.

Tuni dai aka ga wasu daga cikin kungiyoyin sun isa harabar Cocin da rubutaccen sako da amsa kuwwa tare da fara gudanar da zanga-zangar neman a kama Fatoyinbo domin gudanar da bincike a kansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng