JAMB ta damke wani matashi da ya sabunta sakamakonshi daga 153 zuwa 290

JAMB ta damke wani matashi da ya sabunta sakamakonshi daga 153 zuwa 290

-Hukumar JAMB ta kama wani matashi dan shekara 19 bayan da ya sabunta sakamakon jarabawarsa daga 153 zuwa 290

-Dalibin ya canza sakamakon ne bayan da ya hadu da wasu gurbatattu a dandalin sada zumunta na Facebook da suka ce su na gyarawa

-Hukumar ta bayyana cewa tana nan tana kokarin kamo bata garin da ke yaudarar mutane ta yanar gizo suna ansar kudi da sunan za su gyara masu sakamakon

Hukumar jarabawar share fagen shiga jami’a (JAMB) ta kama wani matashi dan shekara 19 da ya sabunta sakamakon jarabawarsa da aka gudanar na wannan shekarar inda ya kara makin sakamakon nashi daga 153 zuwa 290.

An samu tangarda sosai a lokutan da ake yin jarabawar share fagen shiga jami’a ta 2019 wanda hakan ya sanya dalibai da yawa basu samu damar zana jarabawar ba.

Tangardar da aka samu sun hada da matsalolin tantance mutum ta hanyar amfani da zanen yatsunshi, matsalolin sadarwa na yanar gizo, da wasu jarabawowin da aka soke a wasu santocin jarabawar.

Hukumar ta kuma yi koken cewa an samu matsalolin satar amsa daga wajen dalibai wanda hakan ya kawo jinkiri wajen fitar da sakamakon jarabawar duk da cewa hukumar ta yi kokarin dakile satar amsa a lokacin da ake gudanar da jarabawar.

KARANTA WANNAN: Sirrika biyar na cikin dankalin hausa ga lafiyar jiki

Ana zaton cewa matashin dan shekara 19 ya samu haduwa da wasu macuta a dandalin sada zumunta na Facebook da whatsapp, bayan da yaga talla cewa za a iya sabunta ma mutum sakamakonshi na jarabawar Jamb ta 2019.

Sun samu yin nasara a kanshi inda yayi maza ya tuntubi nambar wayar da suka bayar, ya kuma bukacesu da su canza masa sakamakon daga 153 zuwa 290.

Bayan ya tura ma mayaudaran wasu kudade, sai ya rubuta ma hukumar Jamb wasika cewa sun yi kuskure a sakamakon da suka fitar mashi.

Ya kuma tura sakamakon jarabawar na bogi zuwa ga hukumar wanda bayan bincike hukumar ta gano cewa na bogi ne.

Hukumar ta bayyan cewa tana nan tana kokari don ganin an kama mayaudaran da ke hada sakamakon na bogi don a mika su ga hukuma.

Har yanzu dai hukumar na sakin sakamakon jarabawar ta 2019 a hankali a hankali don ganin sun tantance sakamakon.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng