Yunwa ta addabi yan ta'addan Kaduna - Sarkin Birnin-Gwari
-Sarkin Birni Gwari ya bayyana cewa yan ta'addan da ke damun yakinsu basu da isassun makamai da abinci sai ya sanya yanzu basu addabar su
-Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke karbar bakuncin komishinan yan sanda na jihar kaduna
-Sarkin ya kuma yi alkawari ba ma yan sanda duk wata gudunmuwa da suke bukata wajen magance matslolin tsaro a yankin
Sarkin Birnin-Gwari, Zubairu Jibril Maigwari ya bayyana cewa yunwa ta addabi yan ta'addan Kaduna kuma basu da makamai da zasu yi wani babban ta'addanci.
Jibril Maigwari ya bayyana hakan ne a yau Juma'a 28 ga watan Yuni 2019, a lokacin da komishinan yan sanda na jihar Kaduna, Ali Janga ya kai mashi ziyara.
Janga ya ziyarci fadar Maigwari don su tattauna akan matsalolin tsaro a yankin. Sarkin ya bayyana cewa yan ta'addan da ke damun jama'ar karamar hukumar Birnin Gwari basu da isassun makamai shi ya sanya yanzu basu kai hari a ko ina sai wasu kananan wurare kamar kasuwannin kauye.
Ya bayyana cewa yan ta'addan yanzu abincin da zasu ci su rayu kawai suke sata, basu da lokacin da su shiga gari su yi ta kashe mutane.
KARANTA WANNAN: Mun gwammace yan Boko Haram su kashe mu da yunwa ta kashe mu' - Yan gudun hijra
Sarkin ya kuma bayyana cewa“Yanzu muna da karin ofisoshin yan sanda guda uku a karamar hukumar mu, da muna da guda hudu. Yan sandan basu da yawa, ammma suna kokari suna dakkile duk wani ta'addanci da akeyi a yankin.”
"Muna sane da kalubalen da yan sanda ke fuskanta, mun san cewa ba zaku iya turo mana yan sanda a kowanne lokaci ba, amma yan kadan din da ke garemu suna kokari wajen magance duk wani ta'addanci da akeyi a yankinmu.”
“Munyi komishinonin yan sanda da yawa. Na hadu da kusan guda 20 ina kan karaga. Mun basu duk wata gudunmuwa da suke bukata wajen magance matsalolin tsaro a yankinmu. Kuma kaima munyi alkawarin baka duk wani taimako da kake bukata.”
Tun farko, Komishinan ya yabawa sarkin akan irin hadin kai da yake basu wajen ganin su magance matsalolin ta'addanci da sauran laifuffuka a yankin na Birnin Gwari.
Ya ce “Rahotannin da muke samu daga ofisoshinmu na Birnin Gwari abin jin dadi ne. Al'ummar yankinnan na basu hadin kai wajen magance matsalolin tsaro.”
“Muna kara ba mutanen Birnin gwari tabbacin cewa masalar ta'addanci ta kusa zama tarihi a yankin Birni Gwari” A cewar Komishinan.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twittwe: http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng