Allah wadaran naka ya lalace: Wani ya jawo ma kanshi ukuba garin satar wando

Allah wadaran naka ya lalace: Wani ya jawo ma kanshi ukuba garin satar wando

-Kotun majisire ta Modakeke da ke a jihar Osun ta daure wani da ake tuhuma da satar wando tsawon wata shida a gidan yari

-Wanda aka samu da laifin ya bukaci kotun da ta yi mashi sassafci a lokacin zartar da hukuncin

-Amma kotun ta bayyana cewa shi tsohon mai laifi ne kuma baiyi nadama ba, saboda haka bai dace a yi mashi afuwa ba

Kotun Majistire ta Modakeke – Ife da ke jihar Osun ta daure wani tsohon mai laifi, Opayemi Abel dan shekara 24, wata shida a gidan yari saboda ya saci wandon Naira 3,000.

Mai shari’ah Abimbola Famuyide, ya daure mai laifin bayan da ya amsa tuhumar da ake masa ta laifin balle gida da sata.

Mai laifin, wanda mazauni ne a Modakeke a karamar hukumar Ife ta gabas, ya amsa laifuffuka biyun da ake tuhumarsa, daga bisani kuma ya roki kotun da ta yi mashi sassafci.

KARANA WANNAN: An sake bude hanyar Pulka zuwa Gwoza bayan shekaru 5 da rufeta

Alkalin ya daure shi ba tare da zabin ya biya ta ra ba inda ya ce “Shaidun da aka gabatar gaban kotu sun tabbatar da cewa mai laifin tsohon mailafi ne da baiyi nadama ba, saboda haka bai dace a yi mashi sassafci ba.”

“Takardun kotu sun tabbatar da cewa an taba kamashi da laifi aka kulle shi tsawon wata 18 a gidan yari sakamakon satar mashin da yayi shekarar 2017.”

“Dabi’un mai laifin sun nuna cewa bai shirya zama nagari ba, saboda yana da tarihin aikata laifi a baya inda aka kamashi da laifin satar mashin a shekarar 2017.’"

Mai shari’ar ya kara da cewa “Babu yadda za ayi mai laifin ya tafi ba tare da an hukunta shi ba, kuma hukuncin zai zama darasi ga sauran masu san aikata laifi.”

Tun farko dai, yar sanda mai gabatar da kara, sifeta Glory Ona ta gayama kotu cewa mai laifin ya aikata laifin a ranar 25 ga watan Yuni 2019, da misalin karfe 1:00 na dare a unguwar Bossa da ke Modakeke – Ife.

Ona ta bayyana ma kotu cewa ya balle gidan wani Julius Olaboye inda ya sace wando da riga da kudinsu ya kai Naira 4,000

Ta bayyana ma kotu cewa laifin ya saba ma sashe na 383, da 390 da 411 na kundin laifuffuka da hukunce hukuncensu na jihar Osun.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng