An sake bude hanyar Pulka zuwa Gwoza bayan shekaru 5 da rufeta
-An sake bude hanyar Pulka zuwa Gwoza zuwa Limkara bayan sama da shekaru biyar da sojoji suka rufe hanyar sakamakon hare haren Boko Haram.
-Gwamnan jihar ya bayyana cewa an sake bude hanyar ne don yan gudun hijira su samu su yi noma a kakar ruwan saman bana.
-Gwamnan ya kuma yin alkawarin samar da tsaro ga al'ummar yankunan don su yi aikin nomansu cikin zaman lafiya
An sake bude hanyar hanyar da ta fara da ga Pulka zuwa Gwoza ta wuce Limankara, bayan tsawon shekaru biyar da rufe hanyar sakamakon hare haren Boko Haram.
An bude wannan hanyar ne don a samu yan gudun hijira su koma gida don su yi noma a kakar ruwan saman bana.
Jaridar Kanem Trust ta ruwaito cewa za a karfafa ma yan kungiyar kato da gora, mafarauta da yan a kungiyar sa kai ta yadda za su yi aiki da sojojii da yan sanda wajen wanzar da zaman lafiya a garuruwan.
KARANTA WANNAN: Yan sanda sun kama wasu manyan yan fashi 10 a Gwagwalada
Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum da ya duba hanyar ya ce “Zamu basu makamai, mu sa su cikin tsarin albashi kuma mu basu duk abinda su ke bukata.”
“Hanyar na daya daga cikin manyan hanyoyi da suka yi mahada da wasu jihohi hadda kasar kamaru.
“Sojoji sun rufe hanyar tun shekarar 2014 sakamakon hare haren Boko Haram, wanda hakan ya sanya aka daina hada hadar kasuwanci.”
“Harkar kasuwanci, musamman sintirin ababen hawa, zai kawo alfanu sosai, hakan ya sanya muka je da hukumar gyara hanyoyi ta Borno don su duba gadar Limkara."
"Gadar na daya daga cikin hanyoyin da yan Boko Haram su lalata a shekarar 2014. Kuma ina sane cewa hanyar da ta hada Pulka da Gwoza na da matukar mahkimmaci ga al’ummar garuruwan.”
“Za mu shinfida titi daga Pulka zuwa Gwoza da kuma Gwoza zuwa Limkara kuma za a gina gadar nan ta ke – InshaAllah.”
Kanen Trust ta ruwaito cewa an bada kwangilar yin hanyar tun 2010 amma har yanzu ba ayi komi ba bayan sama da shekara tara da bada kwamgilar.
Gwamnan Zulum ya kara da cewa “Za mu tuntubi gwamnatin tarayya don mu tabbatar da cewa an sake duba kwangilar, za mu yi aiki da sojoji don duba yiyuwar yadda mutane zasu koma gonakinsu.’
Gwamnan ya kuma yi alkawarin karfafa ma yan kato da gora, yan kungiyar sa kai, da mafarauta don samar da tsaro ga wandannan garuruwa.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng