Abin da zan yi yanzu bayan ritaya – Wakili Singham

Abin da zan yi yanzu bayan ritaya – Wakili Singham

Muhammad Wakili, tsohon kwamishinan 'yan Sanda na jihohin Katsina da Kano ya cika wata daya da yin ritaya a yanzu.

A hirar da shafin BBC ta yi da shi, ya bayyana cewa har yanzu bai tsaida wani abin yi ba, amma akwai mutanen da suke nemansu ba shi aiki a wani kamfani.

Singham kamar yadda ake kiransa ya kara da cewa zai je Gombe hutu wurin iyayensa.

Tsohon kwamishinan yace: “A lokacin da muka yi ritaya, ranar 26 ko 29 ga wata, Na tafi gida tunda Alhamdulillahi, har yanzu iyayenmu suna da rai kuma suna cikin hayyacinsu da koshin lafiya. Muka je muka ce to Baba mun gama aiki. Mun zo muyi godiya a sa mana albarka, kuma da izininku za mu wuce Umrah. Suka ce inje Umrah sun yadda suka yi mun addu’a.

"Ranar 30 ga wata na tafi Umrah. Da naje Umrah na dawo bayan sati biyu. Daga nan sai na sake zuwa Gombe, sannan naje Kano sannan yanzu na zo Abuja.

“Har yanzu dai ban ban tsayar da abin da zan yi ba. Amma akwai wasu wadanda suke nema su bani aiki na kamfani, amma dai yanzu ina so bayan n agama aunda zan yi a Abuja, zan je Kano nayi bankwaa da Kanawa. Zan je Gombe na zauna da iyaye nakwana biyu kafin ayi tunanin abubuwan da za a yi. In yi zabe idan akwai halin zabi, sannan kuma a ci gaba da rayuwa.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kai mamaya mafakar yan ta’adda, an kama yan kungiyar asiri 53

“Ita rayuwar nan, da ma ya ya balle yanzu ka haura 60, kafa daya na duniya daya na lahira. Dama an ce Mazo SWA y ace 60 ko 70. Ko yanzu aka ce a mutu babu abin mamaki ya zo daidai da nassi ko sunna. Saboda haka babu wani abu da zai tada hankali, sai dai kuma mutum ya yawaita istigfari. Tunda harkar jama’a mutum yayi. Dole ka kuntatawa wani ko ka muzgunawa wani bias kuskure. Amma idan bah aka ba Alhamdulillahi."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng