Kasuwancin kasa da kasa: Lawan ya gana da Jakadan kasar China a Abuja

Kasuwancin kasa da kasa: Lawan ya gana da Jakadan kasar China a Abuja

-Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Lawan Ahmad ya zanta da Jakadan qasar China a Najeriya Mista Zhou Pingjian

-Lawan yayin zantawar ta su ya nemi a daidaita cinikayya tsakanin Najeriya da China

-Inda ya kara da cewa akwai buqatar qasar Chinanta ba wa Shugaba Buhari goyon baya na yinkurin da yake domin bunqasa tattalin arzikin Najeriya

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Lawan Ahmad ya ce, harkar kasuwanci dake tsakanin qasar Najeriya da China na buqatar daidaituwa.

Da yake bayani jiya Laraba a Abuja yayin karbar bakoncin jakadan China a Najeriya, Mista Zhou Pingjian, Lawan ya ce, daidaita lamuran kasuwanci tsakanin kasashen biyu ne kawai zai bada damar samun cinma abubuwan da ake buqata.

KU KARANTA:Saboda tsaro: IG ya sanya karnuka a tashoshin jirgin kasa

A wani zance da mai taimakawa Shugaban majalisar a bangaren yada labarai, Muhammad Isa ya fitar cewa yayi, Shugaban majalisar ya qara da rokon gwamnatin China da ta marawa kokarin da Shugaba Buhari yake yi baya domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

“ Duk da cewa kasar Najeriya da China sun kasance suna alaqa da juna na tsawon lokaci wanda duka kasashen biyu ke amfana da wannan tarayya, amma sai dai abin damuwa shi ne ta yadda a bangaren kasuwanci alaqar ta samu tawaya kadan a yanzu.

“ Yayin da kudin da kayayyakin kasuwancin da Najeriya ke fitarwa zuwa China yake a matsayin biliyan $1.6, kana kuma jimillar kudin kayayyakin da China ke shigowa da su Najeriya ya kama biliyan $12.4. A don haka zai fi kyau idan muka daidaita harkar kasuwancin domin cigaba kasashenmu.” Inji shi.

Ambasada, Pingjian ya jinjinawa Najeriya a kan tsarin da ta qaddamar na ‘One China policy’ inda jakadan ya ce, tabbas wannan tsari ne mai kyau da zai inganta alaqa tsakanin Najeriya da China.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng