Mijina baya haihuwa, wata mata ta shaidawa kotu

Mijina baya haihuwa, wata mata ta shaidawa kotu

-Son haihuwa ya sanya wasu ma'aurata sun rabu da junansu a kotu

-Matar mai suna Habibat ce ta nemi kotu ta bata takardar saki saboda mijinta baya haihuwa

-Matar ta bayyana wa 'yan jarida cewa sun kwashi tsawon shekara biyar tare da mijin nata amma babu labarin haihuwa a don haka ita ta gaji domin ta burin ganin nata yaran

Wata kotun gargajiya wacce ke unguwar Iseyin a cikin jihar Oyo a ranar Laraba ta raba wani aure mai shekaru biyar tsakanin Hafeez da Habibat Imran kan cewa mijin bai haihuwa.

Habibat ita ce ta fara zuwa kotu da neman saki tun a watan Disemban 2018. Lauyan Habibat a kotun ya bayyana kokarin wannan baiwar Allah inda ya nuna cewa ta jima tana hakuri, yanzu kuma ta riga ta gaji saki take nema.

KU KARANTA:Abubuwa 5 da kungiyar Yarbawa ta roki Shugaba Buhari

Matar ta ce: “ Mun kasance tare da shi na tsawon shekara biyar. Tun a wancan lokacin yana iya kokarinsa wurin kwanciya amma sai dai babu labarin haihuwa. A halin yanzu kuwa babu abinda yake iya yi.

“ Ni gaskiya na gaji, hakuri na ya riga ya kare. Kawai abinda yafi dacewa da mu a yanzu shine ya rabu dani, in samu wanda zai iya maida uwar diyansa na aura.”

Ta sake bayyana wa majiyar NAN cewa wannan dalilin ya sanya ta bar gidanta na aure.

A nashi jawabin, Hafeez wanda shi ne mijin nata cewa yayi: “ Ina mai kara bata hakuri kan wannan lamari, mun riga mun saba saboda mun dade tare da da juna. Na kashe kudade masu yawa domin shawo kan wannan matsala, amma abin ya ci tura.

“ Amma idan har taqi amincewa ta tubure a kan cewa lallai sai na sawwake mata, to ta dawo min da wasu daga cikin kayana da tayi gaba da su yayin da take barin gidana.”

Alkalin da ya jagoranci wannan shari’a ya nuna bacin ransa bisa rashin kasancewar Hafeez a kotun, hakan ya sake nuna babu sauran kauna a tsakanin ma’auratan, inji alkalin a don haka ya raba aure tsakaninsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng