Babban magana: Alkali ya daure Boka da dan rakiya a Zariya
Rahotanni sun kawo cewa babbar kotun daukaka kara na shari’an Musulunci da ked a zama a Tudun Wada, Zariya karkashin jaorancin mai shari’a, Alhaji Nuhu Mahmud, ta yake ma wani boka da wani wanda ya ziyarce shi don rufe bakin abokin shari’a, da kuma dan rakiyarsa hukuncin daurin shekara uku.
Da fari dai dan sandan da ya shigar da kara, Abdulhamid Sarki ya bayyana cewa ana zargin mutumin farko da ya fara gabatarwa mai suna Ibrahim Barau, da zuwa wata makabarta a garin Farin Kasa ta karamar hukumar Soba, cikin dare, ida ya binne danyen kwai cikin wani sabon kabari.
Dan sandan ya ci gaba da cewa bayan an kama wanda ake zargin, sai yace wani boka ne ya bashi wannan danyen kwai, kan ya sa a cikin kabari, saboda neman maganin rufe bakin wani mutum da ke shari’a das hi, inda ya bayyana cewa wannan kwai ne zai zamo sanadiyar rufe bakin abokin shari’an nasa.
A nashi banare, bokan mai suna Auwal Abubakar, ya ce, babu shakka, ya ba Ibrahim Barau wannan kwai ne, domin ganin abokin shari’arsa bai sami damar yin magana ba a gaban alkali, a wata shari’a da ya ke yi da wani abokin shari’arsa.
Mai gabatar da karar ya ci gaba da cewa, sai mutum na biyu mai suna Ahmadu Ahmad, wanda ya raka Ibrahim Barau zuwa makabarta domin sa kwai, kamar yadda wannan boka ya umurce shi da ya yi, ya tabbatar wa ‘yan sanda cewar lallai da shi a ka je wannan makabarta domin sa kwai a cikin kabari.
KU KARANTA KUMA: Badakalar makaman Amosun: Babu wani mugun nufi tattare da lamarin – Fadar shugaban kasa
Bayan Alkali Mahmud ya kammala jin bayanin wadanda a ke zargi tare da dukkaninsu su ka amince da zargin da a ke yi ma su, a nan take Alkali ya yanke wa Boka Auwalu Abubakar, dan shekara 25, da Ibrahim Barau, wanda ya cusa kwai a sabon kabari, daurin shekara uku kowannensu su biyu ko kuma tarar Naira 150,000.
Shi kuma dan rakiya zuwa makabarta, Ahmadu Ahmad, alkali ya daure shi wata biyu ko tarar Naira 30,000.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng