Hukumar NDLEA ta damke mutane 186 da miyagun kwayoyi a Jigawa
-Hukumar NDLEA tayi babban kamu a jihar Jigawa
-Mutane 186 hukumar ta kama daga farkon shekarar 2019 kawo wa yanzu
-Babbar kwamandar hukumar a jihar Jigawa, Josephine Ruth Obi ce ta bada wannan bayani yayin da ake taron ranar hana shan kwayoyi ta duniya
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA reshen jihar Jigawa ta bayyana cewa ta kama mutane 186 wadanda ke da sa hannu cikin hada-hadar miyagun kwayoyi a jihar.
Wannan bayanin na kunshe cikin jawabin da Kwamandar hukumar ta jihar Jigawa, Obi Josephine Ruth ta yi a wurin taron ranar hana shan kwaya ta duniya. Taron wanda aka sanya wa taken ‘Lafiya jari, lafiya jari’.
KU KARANTA:Yanzu-yanzu: Tsohon minista, Abubakar Malami ya miqa wa Buhari wani rahoto
Kwamandar ta bayyana cewa: “ Daga watan Junairu zuwa Yuni shekarar 2019, hukumar mu ta yi nasarar damke mutane 186. Daga cikin mutanen 182 maza ne yayin da sauran hudun kuwa mata ne. Mun samu kwayoyi da kuma tabar wiwi a tare da su.”
Har wa yau, Josephine ta cigaba da cewa: “ Akasarin mutanen mun samu kama su ne ta hanyar abokan huldarsu wurin fataucin tabar wiwi da kuma maganin muran nan mai dauke da sinadirin kodin. Sauran kuma sun kasance suna tu’ammali ne da kwayoyi irin su, taramol, diazefam, igzol da dai sauransu.”
Josephine ta jinjina wa gwamnatin Jigawa bisa namijin kokarin da ta yi na bude cibiyar horo ga yara marasa ji musamman wadanda suka fita hayyacinsu a sakamakon tu’ammali da miyagun kwayoyi, inda ta ce wannnan cibiya za ta taimaka kwarai da gaske wurin rage shaye-shaye tsakanin matasa.
Ta kara da cewa, “daga cikin mutanen da aka riga aka kama, akwai 22 wadanda aka tura su gidan kaso yayin da 108 na cigaba da fuskantar shari’a.”
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng